Shugaba Buhari ya mayar da martani ga Bafarawa

Shugaba Buhari ya mayar da martani ga Bafarawa

- Shugaba Buhari ya mayar da martani ga furucin tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa

- Bafarawa dai ya caccaki salon mulkin gwamnatin shugaba Buhari

- Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu ya bayyana cewa Bafarawa bai yi wa Buhari adalci ba domin ya damu da halin da kasar ke ciki

Rahotanni sun kawo cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya mayar da martani ga furucin tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa bayan ya caccaki salon shugabancinsa.

Buhari ya yi martanin ne ta bakin kakakinsa, Malam Garba Shehu a hirar wayar tarho da yayi da majiyarmu ta BBC.

Ya bayyana cewa Bafarawa bai yiwa Shugaban kasar adalci ba akan kalaman da ya yi.

Shugaba Buhari ya mayar da martani ga Bafarawa

Shugaba Buhari ya mayar da martani ga Bafarawa
Source: Depositphotos

Yace: ''Bafarawa ya je ya tambayayi jama'ar jihohin Kaduna da Adamawa da Borno bisa kokarin da Shugaban kasar ya yi a kan lamarin tsaro.

''Abubuwan da ke wakana a hanyar Kaduna, Zamfara da sauran guraren da ke fuskantar hare-haren ta'addanci na damun gwamnati sosai amma kuma a yanzu haka Buhari ya ba sojojin sama da na kasa umarnin zuwa wadannan yankuna domin magance abubuwan da ke damun jama'ar yankunan.''

KU KARANTA KUMA: Sufeto janar na yan sanda da Shugaban DSS sun kai ziyarar aiki hedkwatar rundunar sojin sama (hotuna)

Akan zargin da Bafarawa ya yi kan cewa shugaban bai tattauna da gwamnonin arewa kan ci gaban yankin ba, Malam Garba ya musanta hakan inda ya ce shugaban na tattunawa da gwamnoni lokaci bayan lokaci, a wani zubin kuma yakan bi su har jihohinsu domin tattaunawa dasu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel