Ku fidda cikin matsalolin ku, Tinubu ya fadawa su Tambuwal a Sokoto

Ku fidda cikin matsalolin ku, Tinubu ya fadawa su Tambuwal a Sokoto

Fitaccen dan siyasar nan, tsohon Gwamnan Legas kuma jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Bola Ahmed Tinubu ya fadawa Gwamnan Sokoto da ma jam'iyyar sa ta Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Sokoto su fidda shi cikin matsalolin su.

Tinubu ya yi wannan kalaman ne a cikin wata sanarwar da ya fitar matsayin martani akan wani rubutu da wasu suka yi a jaridun kudi aka kuma wallafa inda a ciki aka zarga da yin katsalandan a harkokin siyasar jihar da ma makwaftan ta na Zamfara da Kebbi.

Ku fidda cikin matsalolin ku, Tinubu ya fadawa su Tambuwal a Sokoto
Ku fidda cikin matsalolin ku, Tinubu ya fadawa su Tambuwal a Sokoto
Asali: UGC

KU KARANTA: An jefar da jaririya da wasika mai sosa zuciya a Kaduna

A cewar tsohon gwamnan na Legas, shi kwarjinin sa da gaskiyar sa hadi da sanin siyasar sa ne kawai ke taimaka masa a siyasar Najeriya amma shi baya katsalandan ko kadan a harkokin da ba a saka shi ba.

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta Najeriya mai zaman kanta dake da alhakin gudanar da zabe a kasar ta mayar wa da kasar Amurka martani akan zarge-zargen da ta yi na cewa zaben da ya gudana ba yi sahihancin da ake tunani can-can ba.

Tun farko dai ofishin jakadancin kasar ta Amurka ya fito da matsayar su ne game da zaben na 2019 da ya gudana a Najeriya in da suka bayyana takaicin su akan yadda suka ce an samu karacin masu kada kuri'u da kuma cinikayyar kuri'a tsakanin 'yan siyasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel