Hukumar sojin kasa ta yiwa manyan dakaru sauye-sauyen aiki

Hukumar sojin kasa ta yiwa manyan dakaru sauye-sauyen aiki

A yayin yunkurin ta na tumke damara da zage dantse wajen tabbatar da ingancin tsaro da kariya da ya rataya a wuyanta, mun samu cewa hukumar sojin kasa ta Najeriya ta yiwa da dama cikin manyan dakarun ta sauye-sauyen aiki.

Shugaban hafsin sojin sama, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai
Shugaban hafsin sojin sama, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai
Asali: UGC

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito da sanadin kamfanin dillancin labarai na kasa, Kakakin rundunar sojin kasa na Najeriya, Kanal Sagir Musa, shi ne ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai a yau Lahadin cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Cikin jerin manyan dakarun soji da guguwar sauye-sauyen wuraren aiki ta kada da su kamar yadda Kanal Musa ya wassafa sun hadar;

Manjo Janar H.O. Otiki

Manjo Janar S.O. Olabanji

Birgediya Janar H.I. Bature

Birgediya Janar T.O. Olowomeye

Birgediya Janar B.A. Muhammad

Birgediya Janar U.M. Bello

Birgediya Janar M.T. Durowaiye

Birgediya Janar S.B. Kumapayi

KARANTA KUMA: Za mu damko maharan jihar Kaduna - Hukumar 'Yan sanda

Birgediya Janar N.M. Jega

Birgediya Janar K.O. Aligbe

Birgediya Janar A.K. Ibrahim

Birgediya Janar G.T.O Ajetunmobi

Birgediya Janar O.G. Onubogu

Birgediya Janar O.M. Bello

Birgediya Janar Z.L. Abubakar

Birgediya Janar A.A Orukotan

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel