Zaben Kano: Gwamnatin Kano ta fara rabawa kananan hukumomi makudan kudade

Zaben Kano: Gwamnatin Kano ta fara rabawa kananan hukumomi makudan kudade

Wata takarda daga gwamnatin jihar Kano ta rabon kudade ya zuwa kananan hukumomi mai kuma dauke da kwanan wata na 12 ga watan Maris dake nuni da wasu kudade da gwamnatin jihar ta Kano ta soma rabawa kananan hukumomin ta, ta soma yawa a kafafen sadarwar zamani.

Kudaden dai ana zargin gwamnatin jihar na raba su ne domin siyen kuri'u da murdiyar zaben gwamnan jihar ne da za'a sake ranar 23 ga watan Maris, kamar dai yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta bayyana.

Zaben Kano: Gwamnatin Kano ta fara rabawa kananan hukumomi makudan kudade
Zaben Kano: Gwamnatin Kano ta fara rabawa kananan hukumomi makudan kudade
Asali: UGC

KU KARANTA: Maganar rikicin siyasar APC a Zamfara ta kara tasowa

Legit.ng Hausa ta samu cewa jumillar kudaden da aka rabawa kananan hukumomin sun kai jumillar Naira miliyan 223 kuma kananan hukumomi 13 ne suka anfana.

Sai dai wani abun da ya daurewa kowa kai shine yadda kusan dukkan kananan hukumomin da suka anfana da rabon kudin za'a iya cewa akwai rumfunan da za'a sake zabe a cikin su.

Kananan hukumomin da aka rabawa kudaden dai sun hada da Bichi, Doguwa, Nassarawa, Rimin-Gado, Gwarzo, Sumaila da Wudil. sauran kuwa sun hada da Dawakin Kudu, Kabo, Dawakin Tofa, Tsanywa, Kumbotso da Kura.

Dukkan su da za su anfana da kudaden da suka kai Naira miliyan 12 zuwa miliyan 24.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel