Da duminsa: Rikicin zabe ya barke a jihar Rivers, an kashe mutane 15

Da duminsa: Rikicin zabe ya barke a jihar Rivers, an kashe mutane 15

- Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samun yanzu na nuni da cewa rikicin siyasa ya barke a jihar Rivers, wanda har ya zama silar mutuwar mutane akalla 15 a jihar

- Legit.ng Hausa ta tattara rahoto kan cewa rikicin ya kawo tsaikon zabe a wuraren da lamarin ya shafa

- An fara gudanar da zaben ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Asabar, inda za a rufe da misalin karfe 2 na rana. Za a kyale wadanda ke kan layi su kad'a kuri'arsu

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samun yanzu na nuni da cewa rikicin siyasa ya barke a jihar Rivers, wanda har ya zama silar mutuwar mutane akalla 15 a jihar. Rahotannin sun bayyana cewa mutanen sun mutu ne a karamar hukumar Akuku Toru da ke jihar.

Legit.ng Hausa ta tattara rahoto kan cewa rikicin ya kawo tsaikon zabe a wuraren da lamarin ya shafa. Yan Nigeria a yau, sun fita kwansu da kwarkwatarsu domin kad'a kuri'arsu a zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya 469.

Wannan na zuwa bayan dage zaben a makon da ya gabata, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi a daren ranar 16 ga watan Fabreru, ranar da ya kamata a gudanar da zaben.

KU KARANTA: KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato

Da duminsa: Rikicin zabe ya barke a jihar Rivers, an kashe mutane 15

Da duminsa: Rikicin zabe ya barke a jihar Rivers, an kashe mutane 15
Source: UGC

A yayin da hukumar INEC ta tsara gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a wannan Asabar din, ta tsara gudanar da taron gwamnoni da 'yan majalisun dokoki, da ma kananan hukumomin babban birnin tarayya Abuja a ranar 9 ga watan Maris.

Zaben zai gudana ne a rumfunan zabe 119,973 da ke fadin kasar, yayin da za a tattara sakamako a cibiyoyin zabe 8,809 da ke gundumomi, kananan hukumomi 774, jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya.

An fara gudanar da zaben ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Asabar, inda za a rufe da misalin karfe 2 na rana. Za a kyale wadanda ke kan layi su kad'a kuri'arsu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel