Zabe: Jam’iyyar PDP ta yi maraba da wanke APC da kotu tayi a Zamfara

Zabe: Jam’iyyar PDP ta yi maraba da wanke APC da kotu tayi a Zamfara

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Zamfara tace tayi amanna da hukunci da kotun daukaka kara ta yankewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Abuja a ranar Alhamis akan shiga cikin masu takara a zaben kasar da za a gudanar.

Dan takaran kujeran gwamna na PDP a jihar, Alhaji Bello Matawalle ya yaba da hakan ne a yayinda yake zantawa da manema labarai akan lamarin.

A cewar shi, wannan ya kasance sakamakon da muka dade muna jira saboda hakan ne zamu gwada mu tabbatar da goyon baya da muke da shi a jihar a matsayin jam’iyya kuma a matsayin al’umma.

Zabe: Jam’iyyar PDP ta yi maraba da wanke APC da kotu tayi a Zamfara

Zabe: Jam’iyyar PDP ta yi maraba da wanke APC da kotu tayi a Zamfara
Source: Depositphotos

Yace, “a matsayinmu na al’umman jihar, mun umurci magoya bayanmu da su cigaba da yin biyayya ga doka sannan kuma su fito suyi zabe cikin kwanciyar hankali.”

Ya bayyana cewa al’umman jihar na tsammanin samun shugabanni masu kula wadanda zasu tabbatar da cigaba a jihar da kuma inganta rayukan al’umma.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta rahoto cewa babban birnin jihar Gusau, sun wayi gari sun tsinci kansu a sabuwar hutun siyasa a ranar Juma’a bayan kotun daukaka kara dake Abuja ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC na da damar shiga zabe da za a gudanar.

Jam’iyyar APC reshen jihar ta fuskanci rikita-rikita tun daga lokacin da jam’iyyar ta gudananr da zaben fidda gwani don zaben wadanda zasu tsaya takara a karkashin jam’iyyar a zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Rundunan yan sanda ta kama jiga-jigan PDP Kebbi da Kwara

NAN ta cigaba da rahoto cewa rikicin ya janyo rabuwar kai a jam’iyyar, bangare daya ta kasance mai biyayya ga gwamnan jihar, Alhaji Abdulazeez Yari sannan dayan bangaren ta kasance dauke da yan takara guda takwas wadanda suka hada da mataimakin gwamna, Ibrahim Wakkala, Ministan Tsaro, Alhaji Mansur Danali da sauransu wadanda aka sani da taken G8.

Ana kyautata zaton cewa hukunci da kotun ta yanke zai kawo karshen rikicin a jam’iyyar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel