Zabe: Jiha daya a kudu, biyu a arewa sun kere ragowar a yawan ma su kada kuri'a

Zabe: Jiha daya a kudu, biyu a arewa sun kere ragowar a yawan ma su kada kuri'a

- Jihar Legas ce ta fi dukkan jihohin Najeriya adadin masu kada kuri'a

- Jihar Kano itace ke biye da Legas a wurin adadin mutanen da suka karbi katin zabe

- Jihohin da ke biye da Kano kuma sune Kaduna da Katsina sai kuma Jihar Rivers

A ranar Alhamis ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta fitar da alkalluman katin zabe da al'umma suka karba gabanin zaben shugaban kasa da za a gudanar a gobe Asabar 23 ga watan Fabrairu.

Kamar yadda alkalumman INEC suka nuna, masu kada kuri'a sun karbi jimilan katin zabe miliyan 72.8 a sassan Najeriya inda jihohin Legas da Kano suke kan gaba.

Shugaban INEC, Mahmood Yakubu ne ya bayar da wannan bayanin a yayin a babban birnin tarayya Abuja.

Zabe: Jiha daya a kudu, uku a arewa sun kere ragowar a yawan ma su kada kuri'a

Zabe: Jiha daya a kudu, uku a arewa sun kere ragowar a yawan ma su kada kuri'a
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Jajiberin zabe: Wani shiri da Atiku ya kulla da jam'iyyu 5 ya samu matsala

Kididigan ya nuna cewa mutane miliyan 5.5 (5,531389) ne suka karbi katin zabe a jihar Legas sai jihar Kano mai biye mata inda mutane miliyan 4.7 (4,696,747) ne suka karbi katin zabe.

Baya ga jihohin Legas da Kano, jihohin Kaduna da Katsina da Rivers ne ke biye da su.

Mutane miliyan 3.6 (3,648,831) ne suka karbi katin zabe a jihar Kaduna, mutane miliyan 3.2 (3,187,988) suka karbi katin zabe a jihar Katsina yayin da jihar Rivers kuma mutane miliyan 2.83 ne suka karbi katin zabe.

Jihohin da ke da karancin wadanda suka karbi katin zabe sune jihar Ebonyi (666,591) sai Bayelsa (769,509) sai kuma jihar Kwara (1,149,969).

Adadin katin zaben da al'ummar ko wace jiha suka karba shine zai nuna adadin kuri'un da za a sa ran samu daga jihohin tunda wadanda su kayi rajista ne kadai za su iya kada kuri'a.

Sai dai idan aka kwantata da abinda ya faru a shekarar 2015, adadin katin zabe da al'umma suka karba baya nufin kowa da ya karbi katin zaben zai jefa kuri'a saboda wasu kawai sun karbi katin zaben ne kuma su kayi zamansu a gidajensu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel