Rundunar hukumar sojin sama sun damke yan bindiga 10 a jihar Kaduna

Rundunar hukumar sojin sama sun damke yan bindiga 10 a jihar Kaduna

Jami'an bataliyan 453 base na hukumar sojin saman Najeriya sun damke wasu yan bindiga goma da muggan makamai da dukiyoyin jama'a.

Yayin hira da manema labarai a ranan Talata a Karina, kwamandan bataliyan 43 Base, Air Commodore Idi Sani ya bayyana yadda jami'an hukumar sukayi arangama da yan bindiga cikin garin Kaduna.

Yace: "A ranan 16 ga watan Febrairu, 2019, wata rundunar soji daga sashenmu a Kaduna tayi arangama da wasu yan baranda masu suna Abdullahi Adamu, Halilu Rilwan, Lawal Hassan, Idris Yusuf, Kabir Muhammad, Badamasi Alhassan da Idris Abubakar rike da muggan makamai a kusada masaukin mahajjata dake unguwar Mando."

"Yan barandan sun yi ikirarin cewa su yan banga ne kuma matafiyane zuwa garin Buruku, karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna."

"A ranan kuma muka damke wani mai suna AbdulRauf Yusuf tare da wani Muhammad Bello cikin wata mota kirar Golf 3."

Bugu da kari, kwamandan ya ce sashen hukumar sojin sama masu yaki da garkuwa da mutane, satan awaki, barandanci sun damke wasu barayin shanaye a dajin RIyawa.

Bayan batakashi da sukayi da jami'an soji, masu kora shanayen sun gudu su bar shanaye 44 da raguna 13.

KU KARANTA: Satar Akwati: Kada ku bi umurnin Buhari - Atiku ya yi kira ga Sojoji

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel