Barayin shanu sun kashe yan farar hula 3 da soja 1 a Katsina

Barayin shanu sun kashe yan farar hula 3 da soja 1 a Katsina

Rahotanni sun kawo cewa a jiya Lahadi, 17 ga watan Fabrairu ne wasu yan bindiga suka kashe yan farar hula uku da soja daya a kauyen Kasai, kimanin kilo 10 zuwa garin Batsari a yankin karaman hukumar Batsari dake a jihar Katsina.

Lamarin, wanda ya auku da misalin karfe 1:00 na tsakar dare yayi sanadiyan raunata mutane da dama sannan aka yi fashin shanaye fiye da 200.

An tattaro cewa yan fashin sun shigo kauyen, sannan suka soma harbe-harbe yayinda yan kauyen suke fafata da su An kawo cewa sojoji sun shiga lamarin daga baya.

Barayin shanu sun kashe yan farar hula 3 da soja 1 a Katsina

Barayin shanu sun kashe yan farar hula 3 da soja 1 a Katsina
Source: UGC

Yayinda yake tabbatar da lamarin, mai magana da yawun yan sandan reshen, Gambo Isah, yace yan bindigan wadanda suka zo daga jejin Rugu, sun kai farmaki kauyen kafin kaiwa rundunan soja harin bazanta inda suka kashe soja daya.

KU KARANTA KUMA: An samu rabuwar kai a APC reshen Benue kan kudaden kamfen din shugaban kasa

Yace kwamishinan yan sanda, Sanusi Buba, ya ziyarci kauyen don nuna jaje ga al’umman da nuna tausayinsa akan wadanda suka ji rauni.

Yayinda yake musanta fashin shanaye, Isah yace yan fashin sun kai gid hari gidaje inda suka tafi da kudade da wayoyi.Yace an inganta matakan tsaro a garin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel