Dage zaben 2019: Atiku ya kwancewa Buhari, APC da INEC zani a kasuwa, ya ja hankalin 'yan Nigeria

Dage zaben 2019: Atiku ya kwancewa Buhari, APC da INEC zani a kasuwa, ya ja hankalin 'yan Nigeria

- Alhaji Atiku Abubakar, ya bukaci 'yan Nigeria da su kasance masu daukar hakuri akan wannan mataki da hukumar INEC ta dauka na dage zaben shugaban kasar

- Atiku ya ce abun takaici ne ace gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza yin amfani da dogon lokacin da ta samu wajen shiryawa zaben

- Ya ta'allaka wannan mataki na INEC da karin maganar nan ta "Biri da shan duka, gardi da karbar kudi"

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bukaci 'yan Nigeria da su kasance masu daukar hakuri akan wannan mataki da hukumar zabe mai zaman kanta ya kasa INEC ta dauka na dage zaben shugaban kasar.

Atiku ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya sawa hannu da kansa a safiyar ranar Asabar, a matsayin martani kan matakin da INEC ta dauka na dage babban zaben kasar kamar yadda shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar.

Atiku ya sa hannu akan sanarwar a matsayin jawabi kai tsaye ga 'yan Nigeria, daga Yola, jihar Adamawa inda ya koma domin kad'a kuri'arsa.

KARANTA WANNAN: PDP ta yi tur da dage zaben shugaban kasa, ta zargi APC da sa hannu a matakin INEC

Dage zaben 2019: Atiku ya kwancewa Buhari, APC da INEC zani a kasuwa, ya ja hankalin 'yan Nigeria
Dage zaben 2019: Atiku ya kwancewa Buhari, APC da INEC zani a kasuwa, ya ja hankalin 'yan Nigeria
Asali: Facebook

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce abun takaici ne ace gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza yin amfani da dogon lokacin da ta samu wajen shiryawa zaben.

Ya ta'allaka wannan mataki na INEC da karin maganar nan ta "Biri da shan duka, gardi da karbar kudi."

Atiku ya shawarci 'yan Nigeria da su rungumi zaman lafiya tare da danne zuciyarsu akan yin fushi da wannan mataki, yana mai cewa "Zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana ha maza ha mata sai ya yi."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel