Dandalin Kannywood: Jaruma Fati KK ta bar tafiyar Atiku ta koma ma Buhari

Dandalin Kannywood: Jaruma Fati KK ta bar tafiyar Atiku ta koma ma Buhari

Dai dai lokacin da jarumai a masana'antar shirya fina finan Hausa ke ta kara tsunduma kan su a cikin harkokin siyasa, ana cigaba da samun sauyin sheka daga wata jam'iyya zuwa wata a tsakanin jaruman, mazan su da matan su.

A yau ma mun samu labarin cewa daya daga cikin fitattun jaruman na Kannywood mata, mai suna Fati KK ta shelanta sauya shekar ta daga tafiyar dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar adawa ta PDP watau Alhaji Atiku Abubakar.

Dandalin Kannywood: Jaruma Fati KK ta bar tafiyar Atiku ta koma ma Buhari
Dandalin Kannywood: Jaruma Fati KK ta bar tafiyar Atiku ta koma ma Buhari
Asali: UGC

KU KARANTA: Kafin karfe 12 na ranar Asabar Buhari ya sha kasa

Haka zalika Fati KK ta bayyana cewa ita yanzu ta koma tafiyar dan takarar shugabancin kasar Najeriya a karkashin jam'iyyar APC watau Muhammadu Buhari.

A baya dai mun kawo maku cewa daya daga cikin fitattun fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Maryam Gidado wadda aka fi sani da Maryam Babban Yaro ta bi bayan jarumi Adam A. Zango inda ta bayyana goyon bayan ta ga jarumin game da sauya shekar da yayi a siyasance.

A cewar ta, ko kusa bai kamata mutane su ga laifin jarumin ba domin kuwa kowa yanayin siyasa ne domin ya samu wani abu kuma ya samu kima da daraja musamman ma a wurin mutanen da ake yi domin su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel