APC zuwa PDP: Jaruma Maryam Gidado tayi kaca-kaca da masu sukar Adam A. Zango

APC zuwa PDP: Jaruma Maryam Gidado tayi kaca-kaca da masu sukar Adam A. Zango

Daya daga cikin fitattun fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Maryam Gidado wadda aka fi sani da Maryam Babban Yaro ta bi bayan jarumi Adam A. Zango inda ta bayyana goyon bayan ta ga jarumin game da sauya shekar da yayi a siyasance.

A cewar ta, ko kusa bai kamata mutane su ga laifin jarumin ba domin kuwa kowa yanayin siyasa ne domin ya samu wani abu kuma ya samu kima da daraja musamman ma a wurin mutanen da ake yi domin su.

APC zuwa PDP: Jaruma Maryam Gidado tayi kaca-kaca da masu sukar Adam A. Zango
APC zuwa PDP: Jaruma Maryam Gidado tayi kaca-kaca da masu sukar Adam A. Zango
Asali: Facebook

KU KARANTA: Diyar Buba Galadima ta halaci kamfe din Buhari

Tun farko dai jarumin ya sanar da dalilin sa na sauya shekar daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP inda yace a da yana yin siyasar ce ba tare da wata darattawa ba daga wajen wadanda yake yi domin su duk kuwa da irin tasirin sa.

Mai karatu dai zai iya tuna mun kawo maku labarin cewa Adam A Zango na gab da watsa ma shugaban kasa Muhammadu Buhari kasa a ido, ta hanyar shekewa zuwa bangaren siyasar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wata majiya dake kusa da Zango ce ta tabbatar da haka, inda majiyar tace Zango ya yanke shawarar jefar da kwallon mangwaro domin ya huta da kuda ne bayan wata ganawar sirri da yayi da wasu makusanta Atiku Abubakar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel