Bayan tafiyar Buhari: Yan ta'adda sun farwa tawagar gwamnan jihar Taraba, Ishaku

Bayan tafiyar Buhari: Yan ta'adda sun farwa tawagar gwamnan jihar Taraba, Ishaku

- Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu na nuni da cewa wasu 'yan ta'adda sun farwa tawagar gwamnan jihar, Darius Ishaku

- Yan ta'addan, kamar yadda rahotanni suka bayyana, sun lalata wasu daga cikin ababen hawar tawagar da suka hada da motar mataimakin gwamnan jihar

- A cewar hadimin gwamnan, harin ya faru ne karkashin umurnin jam'iyyar adawa da nufin haddasa rikici a jihar gabanin babban zaben 2019

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu na nuni da cewa wasu da ake kyautata zaton cewa mambobin jam'iyyar adawa ne a jihar Taraba, a yammacin ranar Alhamis, sun farwa tawagar gwamnan jihar, Darius Ishaku a kan hanyarsa ta komawa cikin gari bayan raka shugaban kasa Muhammadu Buhari filin sauka da tashi na jiragen sama na jihar.

Yan ta'addan, kamar yadda rahotanni suka bayyana, sun lalata wasu daga cikin ababen hawar tawagar da suka hada da motar mataimakin gwamnan jihar, Haruna Manu.

Mai tallafawa gwamnan na musamman kan harkokin watsa labarai, Bala Dan Abu ya tabbatar da faruwar hakan a zantawarsa da manema labarai a daren ranar Alhamis.

KARANTA WANNAN: Debo ruwan dafa kai: Wani dan sanda ya harbe dan acaba har lahira saboda siyasa

Bayan tafiyar Buhari: Yan ta'adda sun farwa tawagar gwamnan jihar Taraba, Ishaku

Bayan tafiyar Buhari: Yan ta'adda sun farwa tawagar gwamnan jihar Taraba, Ishaku
Source: Depositphotos

A cewar hadimin gwamnan, harin ya faru ne karkashin umurnin jam'iyyar adawa da nufin haddasa rikici a jihar gabanin babban zaben 2019.

Ya ce: "An farwa tawagar gwamna Darius Ishaku akan hanyarsa ta barin filin tashi da sauka na jiragen sama, inda gwamnan da mataimakinsa da sauran manyan jami'an gwamnatin suka yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari rakiya.

"Yan ta'addan sun lalata motar mataimakin gwamnan da sauran wasu motoci masu yawa da ke cikin tawagar, da suka hada da motar kwamishin 'yan sanda na jihar da kuma motar mai baiwa gwamnan shawara na musamman."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel