Wasu yan iska sun lalata hotunan kamfen din Buhari a Taraba

Wasu yan iska sun lalata hotunan kamfen din Buhari a Taraba

Wasu mutane da ake zargin yan iska ne daga jam’iyyar adawa sun lalata manyan hotunan kamfen din Shugaban kasa Muhammadu Buhari da na jam’iyyarsa a jihar Taraba gabannin ziyarar da Shugaban kasar ke shirin kaiwa Jalingo, babbar birnin jihar.

Wasu da ake zargin yan iska ne sun lalata manyan hotunan kamfen din Shugaban kasa gabannin ziyarar kamfen dinsa a Jalingo.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ana sanya ran Shugaban kasa Buhari zai kai ziyara jihohin Adamawa da Taraba a ranar AAlhamis, 7 ga watan Fabrairu.

Wasu yan iska sun lalata hotunan kamfen din Buhari a Taraba
Wasu yan iska sun lalata hotunan kamfen din Buhari a Taraba
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa wani majiya daga jamiyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyna cewa Shugaban kasar ya bukaci mambobin APC a jihar da kada su rama samma su ci gaba da gudanar da harkokin kamfen dinsu cikin kwanciyar hankali da lumana.

Wasu yan iska sun lalata hotunan kamfen din Buhari a Taraba
Wata majita ta APC ta zargi PDP da aikata hakan
Asali: UGC

A halin da ake ciki, shugaba Muhammadu Buhari ya dira filin kwallon Jolly Nyame da ke garin Jalingo, babban birnin jihar Taraba a ranan Alhamis, 7 ga watan Febrairu, 2019 domin yakin neman zabensa na karo biyu da za'a gudanar nan da kwanaki 9.

KU KARANTA KUMA: Daga yanzu za a dunga ba jamian soji kula irin wacca ake ba manyan mutane a filin jirgi – Ministan sufurin sama

Shugaban kasan ya cigaba da yakin neman zabensa ne a yau bayan kammala taron yankin Yarbawa da Inyamurai face jihar Legas.

Bayan kammala taro a Taraba, shugaba Buhari zai garzaya mahaifar Alhaji Atiku Abubakar, jihar Adamawa, domin kamfe.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel