Umurnin Buhari: Jerin sunayen kamfanoni 6 da zasu gina hanyoyi 19 a fadin tarayya, Dangote ne na daya

Umurnin Buhari: Jerin sunayen kamfanoni 6 da zasu gina hanyoyi 19 a fadin tarayya, Dangote ne na daya

Sakamakon yanke shawarar shugaba Muhammadu Buhari, wasu kamfanonin Najeriya shida masu zaman kansu zasu ginawa yan Najeriya hanyoyi 19 a fadin jihohin tarayyar Najeriya.

Shugaba Buhari ya rattabba hannu kan takardar umurni wacce zata baiwa kamfanoni masu zaman kansu damar ginin sabbin hanyoyi da kuma gyara wasu a dukkan sassan Najeriya.

Wannan mataki da shugaban kasa ya dauka zai kawo inganci da rage almubazzarancin da ma'aikatan gwamnati keyi wajen baiwa yan kwangila aiki. A maimakin kudin harajin da kamfanonin zasu biya, su ginawa al'umma hanyoyi da shi.

Kalli jerin sunayen kamfanonin:

1. Kamfanin Dangote

2. Kamfanin iskar gas (NLNG),

3. Lafarge Africa Plc

4. Unilever Nigeria Plc

5. Flour Mills of Nigeria Plc

6. China Road and Bridge Corporation

KU KARANTA: Lafiya: Amfani da Tumatir gwalgwaji na janyo cutar daji - Masana

Wadannan kamfanoni shida zasu gina hanyoyi 19 wanda yayi jimillan kilomita 794.4 a jihohi 11.

A taron rattaba hannu kan wannan takarda, shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana ceewa wannan mataki da Buhari ya dauka zata taimakawa gwamnatin wajen tattalin biliyoyin naira.

Yace: Wannan mataki babba ne saboda zai baiwa kamfanoni masu zaman kansu daman amfani da kudinsu, iya aikinsu, da kokarinsu wajen gina hanyoyi cikin lokaci da gwamnatin Najeriya za tayi tattalin biliyoyin kudade."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel