Labarin wata mata da tsutsotsi ke fita daga jikin ta kullum a Najeriya

Labarin wata mata da tsutsotsi ke fita daga jikin ta kullum a Najeriya

Hausawa dai na cewa in-da-ranka zaka sha kallo a duniyar nan kuma indai ba mutum ya koma ga mahaliccin sa ba, to bai gama ganin abubuwan mamaki ba ko kadan a rayuwar sa. Haka zalika wasu abubuwan dake faruwa a kusa damu ba su ma misaltuwa.

Yau dai muna dauke ne da wani labari mai sosa zuciya na wata mata da kawar ta ta labarta cewa wasu irin halittu masu kama da tsutsotsi dake fita daga jikin ta a kullum rana kuma har asibiti taje amma basu samu magani ba.

Labarin wata mata da tsutsotsi ke fita daga jikin ta kullum a Najeriya

Labarin wata mata da tsutsotsi ke fita daga jikin ta kullum a Najeriya
Source: Facebook

KU KARANTA: Bayan rikitowa daga jirgi, Osinbajo yayi magana

Legit.ng Hausa ta samu cewa kawar matar mai suna Jennifer Obi ce dai ta labarta labarin matar a wani dandalin tattaunawa na kafar sadarwar zamni ta Facebook mai suna Once a mum, always a mum (OMAM).

Jennifer Obi ta cigaba da cewa kawar ta ta wadda keda shekaru 30 da 'yan kai a duniya tana cikin mawuyacin hali saboda larurar dake tare da ita kuma tana matukar bukatar taimakon al'umma sannan kuma suna neman dukkan mai shawara ko taimako da ya taimaka masu.

Ta cigaba da cewa suna bukatar addu'a daga daukacin al'ummar kasar domin kuwa lamarin yana basu tsoro. A cewar ta matar wadda ta sakaya sunan ta tsutsotsin akalla 6 zuwa 10 ne ke fita daga jikin ta a kullum.

Ga dai hoton nan:

Labarin wata mata da tsutsotsi ke fita daga jikin ta kullum a Najeriya

Labarin wata mata da tsutsotsi ke fita daga jikin ta kullum a Najeriya
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel