APC ta yi babban kamu a Sokoto inda Sifawa da yan PDP 6441 suka koma jam’iyyar

APC ta yi babban kamu a Sokoto inda Sifawa da yan PDP 6441 suka koma jam’iyyar

A ci gaba a sauye-sauye sheka da ake yi zuwa jam’iyyar All Progressives Congress ( APC ), a jihar Sokoto, wani tsohon mataimakin kwanturola na hukumar Fursuna na Najeriya, Alhaji Umaru Yari Sifawa, da wasu yan PDP 6441 sun sauya sheka zuwa APC a ranar Laraba, 30 ga watan Janairu.

Hakan na kunshe ne a wani jawabi dauke da sa hannun mai ba Sanata Aliyu Magatakarda Wammako shawara a kafofin watsa labarai, Bashir Rabe Mani, Dan Masanin Mani zuwa ga manema labarai a Sokoto.

Jawabin ya bayyana cewa sabbin masu sauya shekar sun samu tarba a APC daga hannun Shugaban jam’iyyar a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a lokacin kamfen dinta a garuruwan Yabo da Bodinga, hedkwatan Yabo da kuma karamar hukumar Bodinga da ke jihar.

APC ta yi babban kamu a Sokoto inda tsohon DC na fursuna da yan PDP 6441 suka koma jam’iyyar
APC ta yi babban kamu a Sokoto inda tsohon DC na fursuna da yan PDP 6441 suka koma jam’iyyar
Asali: Twitter

A Bodinga yan PDP 3155 ne suka koma APC, ciki harda wani tsohon mataimakin kwanturola na hukumar Fursuna na Najeriya, Alhaji Umaru Yari Sifawa mai ritaya da kuma wani tsohon kakakin karamar hukumar Bodinga, Alhaji Bello Dandari da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Katsina, Daura za su samu asibitin koyarwa da FMC

Sifawa yace sun koma APC ne duba ga tarin adalci da daidaiton da ke ciki, da kuma tarin nasarorin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu.

Ya bukaci tsoffin abokansu da ke PDP har yanzu da su yi gaggawan dawowa APC kafin lokaci ya kure masu.

A Yabo, yan PDP 3287 ne suka koma APC, inda suka bayyana nasarorin shugaba Buhari da Sanata Wamakko a matsayin hujjarsu ta sauya sheka zuwa jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel