An kubutar da mutane 61 daga hannun Boko Haram

An kubutar da mutane 61 daga hannun Boko Haram

A yayin wasu farmakai da dakarun Najeriya suka kai sun kubutar da mutane 61 da ‘yan ta’addar Boko Haram suka yi garkuwa da su.

Mataimakin Kakakin Rundunar Sojin Najeriya Kanal Onyeama Nwachukwu ya fadi cewar sun kai farmakai kan ‘yan ta’addar Boko Haram a yankunan Mafa da Dikwa dake arewacin jihar Borno.

An kubutar da mutane 61 daga hannun Boko Haram
An kubutar da mutane 61 daga hannun Boko Haram
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zakzaky: 'Yan shi'a sun yi wa Gwamnatin Buhari Al-qunutu

Nwachukwu ya kara da cewa, a yayin farmakan an kubutar da mata 37 da yara kanana 24 daga hannun ‘yanta’addar na Boko Haram, kuma an kashe mambobinsu 15.

Nwachukwu ya kuma ce, an jikkata soja 1 sakamakon harin.

Ashekarun 2000 ne aka kafa kungiyar ta’adda ta Boko Haram inda tun 2009 ta fara kai hare-hare wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu 20.

Daga shekarar 2015 zuwa yau kungiyar ta tsaurara kai hare-hare a kasashen dake makotaka da Najeriya da suka hada da Kamaru, Chadi da Nijar.

Kungiyar Boko Haram ta kashe akalla mutane 2 a yankin tafkin Chadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel