Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga yanzu haka na barin wuta a barikin sojojin jihar Yobe

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga yanzu haka na barin wuta a barikin sojojin jihar Yobe

Yayin da ake kasa da awanni 24 da ake dakun zuwan shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a jihar Yobe, mun samu labarin cewa yanzu haka wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne na barin wuta a barikin sojojin jihar dake a garin Buni Yadi.

Barikin wanda ke zaman daya daga cikin makarantu na musamman na koyon dubarun yakin sojojin dai mun samu labarin cewa tun wajen karfe 5 na yammacin ranar Asabar ne suke ta bata kashi da 'yan ta'addan.

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga yanzu haka na barin wuta a barikin sojojin jihar Yobe
Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga yanzu haka na barin wuta a barikin sojojin jihar Yobe
Asali: Twitter

KU KARANTA: Abu ne mai wuya in fadi zabe - Buhari

Legit.ng Hausa ta samu cewa wasu da suka ga zuwan 'yan ta'addan sun bayyanawa majiyar mu cewa sun shiga barikin ne da gudun tsiya cikin wasu manyan motoci kirar Hilux guda 5 makare da muggan makamai da gurneti.

Ganau din ya cigaba da cewa mayakan da suka zo da yawan gaske sun yi ta daga muryar su tare da kabbarori wanda hakan ya sa dukkan al'ummomin farar hula da suka ga hakan sai suka nemi mafaka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng