Fatattakar 'yan ta'adda: Rundunar sojin sama ta tura jirgin yakin sama da dakaru zuwa Sokoto
- Rundunar sojin sama ta Nigeria (NAF) a ranar Asabar, ta aike da wani jirgin yakin sama, tare da kayayyakin yaki, da kuma wata rundunar dakarunta na musamman (SF) a jihar Sokoto
- Haka zalika tura jirgin yakin, kayan yakin, da kuma dakarun sojin zai taimaka wajen yunkurin da ake yi na kawo karshen matsalolin tsaro da jihohin Sokoto da Zamfara
- Jawabin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Air Commodore Ibinkule Daramola, daraktan hulda da jama'a da watsa labarai na rundunar sojin sama
Rundunar sojin sama ta Nigeria (NAF) a ranar Asabar, ta aike da wani jirgin yakin sama, tare da kayayyakin yaki, da kuma wata rundunar dakarunta na musamman (SF) a jihar Sokoto domin bunkasa yaki da 'yan ta'adda da barayin shanu a shiyyar Arewa maso Yammacin kasar karkashin atisayen DIRAN MIKIYA.
Haka zalika tura jirgin yakin, kayan yakin, da kuma dakarun sojin zai taimaka wajen yunkurin da ake yi na kawo karshen matsalolin tsaro da jihohin Sokoto da kuma iyakokin Zamfara da Sokoto ke fuskanta.
Jawabin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Air Commodore Ibinkule Daramola, daraktan hulda da jama'a da watsa labarai na rundunar sojin sama, inda kuma bayyana cewa babban jami'in horas da soji na rundunar, Air Vice Marshal Oladayo Amao ne ya karbi kayayyakin da aka tura, inda ya bukaci dakarun da su zage damtse a yayin gudanar da ayyukansu.
KARANTA WANNAN: Duba matakan da zaka bi domin yin rejistar 2019 UTME - JAMB

Asali: Facebook
Daga cikin wanda ya karbi kayan da dakarun sojin akwai kwamandan rundunar hadin guiwa ta shirin DIRAN MIKIYA, Air Commodore Ayoola Jolasinmi, da kuma kwamnandan sansanin rundunar gaba ta 119 FOB, Air Commodore Jibrin Usman.
Idan za a iya tunawa, bayan da rundunar sojin sama ta kasa NAF da ke jihohin Katsina, Zamfara da Sokoto a ranar 26 ga watan Disamba, ta dauki kudurin bunkasa filin jirgin Sultan Abubakar III domin rinka tura dakaru, kayayyakin rundunar sojin saman, to yanzu dai za a iya cewa shirin hakan yayi nisa, wanda kuma zai taimaka wajen kawo karshen ta'addancin 'yan bindiga, barayin shanu, masu garkuwa da mutane da dai sauran nau'i na ta'addanci.
Duba hotunan jirgin yaki, kayayyakin yaki da kuma dakaru na musamman da rundunar sojin saman ta tura jihar Sokoto.

Asali: Facebook

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng