Da dumi duminsa: Yan bangar siyasa sun farwa Titi matar Atiku, ta sha da kyar

Da dumi duminsa: Yan bangar siyasa sun farwa Titi matar Atiku, ta sha da kyar

- Wasu da ake kyautata zaton 'yan bangar siyasa ne, sun farwa matar Alhaji Atiku Abubakar, Titi a gidan Sarkin Sasa, yankin Ojoo da ke Ibadan cikin jihar Oyo

- Wanda lamarin ya afku gabansa ya bayyana cewa Titi, ta tattauna da Sarkin Sasa da kuma al'ummar Hausawa da ke a yankin, sa'ilin da aka kai mata farmakin

- Wani jigo a jam'iyyar PDP a jihar, Alhaji Bisi Olopoenia, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya bayyana cewa jam'iyyar ta fara bincike don gano wadanda suka kai harin

A yammacin ranar Juma'a, wasu da ake kyautata zaton 'yan bangar siyasa ne, sun farwa matar tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, Titi a gidan Sarkin Sasa, yankin Ojoo da ke Ibadan cikin jihar Oyo.

Mrs. Abubakar ta isa jihar ne tun kwanaki biyu da suka gaba domin nemawa mijinta amincewar al'ummar jihar, kan zabensa a ranar 16 ga watan Fabreru, 2019.

Wanda lamarin ya afku gabansa ya shaidawa jaridar Punch cewa ta tattauna da Sarkin Sasa da kuma al'ummar Hausawa da ke a yankin, sa'ilin da yan bangar siyasar suka farwa tawagarta.

KARANTA WANNAN: HOTUNA: Dandazon al'ummar jihar Kaduna sun yi dafifi domin jiran isowar Buhari

Da dumi duminsa: Yan bangar siyasa sun farwa Titi matar Atiku, ta sha da kyar
Da dumi duminsa: Yan bangar siyasa sun farwa Titi matar Atiku, ta sha da kyar
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa waus daga cikin magoya bayan mijin nata, da suke mata rakiya, sun samu raunuka a yayin harin.

Wani jigo a jam'iyyar PDP a jihar, Alhaji Bisi Olopoenia, ya tabbatar bda faruwar harin, inda ya bayyana cewa jam'iyyar ta fara bincike don gano dalili da kuma wadanda suka kai harin ga bakin, wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Ya ce akwai rahotannin da suka samu na cewar 'yan bangar siyasar sun bukaci kudi daga bakin, bayan kuma an basu ne, wasu daga cikinsu suka ci gaba da neman tayar da rikici a wajen, wanda har ta kai sun raunata wasu daga cikin bakin.

Duk wani yunkuri na jin ta bakin mai mamgana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar, Adekunle Ajisbutu ya ci tura, har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan labarin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel