Daga karshe: Shelkwatar tsaro ta kasa ta sanar da ranar binne gawar Alex Badeh

Daga karshe: Shelkwatar tsaro ta kasa ta sanar da ranar binne gawar Alex Badeh

- Shelkwatar taro ta Nigeria, ta sanar da ranar binne gawar tsohon shugaban dakarun soji na kasa, Air Chief Marshal Alex Badeh

- Birgediya Janar Agim ya ce za a gudanar da jana'izar ne a ranar Laraba, 23 ga watan Janairu bayan gudanar da ibada a coci

- Tsohon shugaban dakarun soji na kasar ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da wasu 'yan bindiga suka bude masa wuta yana kan hanyar komawa Abuja daga Kebbi

Rahotannin da muka samu daga gidan talabijin na Channel na nuni da cewa shelkwatar rundunar tsaron Nigeria, a ranar Juma'a, 18 ga watan Janairu, ta bayyana cewa ta sanya ranar da za a binne gawar tsohon shugaban dakarun sojin kasar, Air Chief Alex Badeh.

Sanarwar jana'izar na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mukaddashin daraktan watsa labarai na rundunar tsaron, Birgediya Janar John Agim inda ya ce za a fara gudanar da shirye shiryen bison gawar ne zai fara a ranar Lahadi da wakokin rundunar soji da za a gudanar a cocin Protestant da ke cikin sansanin rundunar sojin sama na Abuja.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Jam'iyyun siyasa sun bakado wani shiri na cafke Onnoghen a ranar Talata

Daga karshe: Shelkwatar tsaro ta kasa ta sanar da ranar binne gawar Alex Badeh
Daga karshe: Shelkwatar tsaro ta kasa ta sanar da ranar binne gawar Alex Badeh
Asali: Twitter

Birgediya Janar Agim ya kuma bayyana cewa ayyukan da za a gudanar na binne gawar tsohon shugaban dakarun tsaron kasar sun hada da wata addua ta musamman da za a gudanar a yayin bauta a cocin a ranar Laraba, 23 ga watan Janairu.

Da rana ne ake sa ran binne gawar Alex Badeh a babbar makabarta ta jami'an soji da ke Abuja.

A baya dai Legit.ng Hausa, ta ruwaito maku cewa wasu 'yan bindiga sun harbe tsohon shugaban rundunar tsaron kasar Air Chief Marshal Alex Badeh, a kan hanyarsa ta komawa gida Abuja bayan kai ziyara gonarsa a Kebbi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng