An samu bambancin ra'ayi tsakanin gwamnatin tarayya da wasu manyan kungiyoyi 3 kan sankame asusun Alkalin Alkalai
Ba bu wata shiga da farau-farau zai yi wajen bai wa koko tsoro domin kuwa a halin yanzu ba bu wani boyayyen lamari dangane da dambarwa gami da cecekucen da ke ci gaba da gudana kan yunkurin gwamnatin tarayya na maka alkalin alkalan Najeriya, Mai shari'a Walter Onnoghen a gaban babbar kotun dabi'u ta kasa wato CCT.

Asali: UGC
Dambarwar ta biyo bayan kiraye-kirayen gwamnatin tarayya na neman alkalumma na shari'a da kuma dokokin kasa su yi tasiri wajen hukunta alkalin alkalai sakamakon zargin sa da rashin bayyana adadin dukiyar da ya mallaka yayin karbar ragamar jagorancin kujerar sa ta babban alkali.
A sanadiyar haka, gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin sankame asusai biyar na ajiyar kudi da ke bankin Standard Chattered mallakin Alkali Onnoghen yayin da ake ci gaba da kiradadon hukuncin da shari'a za ta zartar a kansa.
Umarni na haramtawa babban alkalin damar ribatar asusan sa na ajiyar kudi ya bayu ne da sa hannun lauyan kolu kuma ministan shari'a na kasa, Abubakar Malami, da ya shimfida cikin wata wasika mai dauke da lambar HAGF/2019/E06/Vol.01 tare da kwanan wata na 14 Janairu, 2019, zuwa ga shugaban hukumar gudanar da al'amurran kudi na kasa.
Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, yayin bukatar a sakaya sunan sa, wani babban jami'i da ke aiki a babbar ma'aikatar shari'a ta kasa, shine ya shaidawa manema labarai asali da kuma tushen wannan umarni da ya kasance lauyan kolu na Najeriya.
KARANTA KUMA: Arewa na goyon bayan sauya fasalin kasa 100 bisa 100 - El-Rufa'i
A yayin da kungiyar kawo sauyi ta Najeriya mai taken Coalition for Change in Nigeria ke shawartar Alkali Onnoghen da ya yi murabus domin tsare mutunci, wasu manyan kungiyoyi 3 sun ja daga wajen zayyana wa gwamnatin tarayya rashin amincewar su da wannan lamari da suka misalta a matsayin cin kashi da kuma kwatar 'yancin babban alkalin na kasa.
Bisa ga furucin wakilan su, kungiyoyin uku da suka bayyana ra'ayin su da ya sha bamban da na gwamnatin tarayya sun hadar da kungiyar hadin kan jam'iyyun siyasa na Najeriya ta CUPP, Coalition of Political Parties, Cibiyar lauyoyin Najeriya ta NBA, Nigerian Bar Association, da kuma kungiyar manyan lauyoyi ta SAN, Senior Advocates of Nigeria.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng