Maimuna Aliyu, mahaifiyar Maryam Sanda ta sake shiga sabuwar tsomomuwa

Maimuna Aliyu, mahaifiyar Maryam Sanda ta sake shiga sabuwar tsomomuwa

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu aikata laifuka da suka jibinci cin hanci da rashawa watau Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) a turance ta gurfanar da Maimuna Aliyu gaban kuliya kan badakalar $360,000.

ICPC din dai tana tuhumar Maimuna Aliyu din dake zaman tsohuwar shugabar bankin adashen gata na Aso Savings and Loans Plc da karkatar da zunzurutun kudaden da suka kai $360,000 ta bankin a shekarar 2012 da ta gabata.

Maimuna Aliyu, mahaifiyar Maryam Sanda ta sake shiga tsabuwar tsomomuwa
Maimuna Aliyu, mahaifiyar Maryam Sanda ta sake shiga tsabuwar tsomomuwa
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: APC ta nada sabon shugaba a kudancin Najeriya

Legit.ng Hausa ta samu cewa sai dai da aka karantawa wadda ake tuhumar laifin da ake zargin ta, ta musanta zargin sannan kuma lauyan ta ya nemi a bada ita beli kafin a soma shari'ar.

Daga karshe dai alkalin kotun ta bayar da belin wadda ake tuhumar sannan kuma ya saka 6 ga watan Fabreru a matsayin ranar da za'a cigaba da shari'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng