Sanata Shehu Sani: Babu wani abun kirki da El-Rufai ya tsinanawa Kaduna

Sanata Shehu Sani: Babu wani abun kirki da El-Rufai ya tsinanawa Kaduna

- Shehu Sani, ya bayyana gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin wanda bai tsinanawa jihar Kaduna komai ba, tsawon kusan shekaru 4 na mulkinsa

- Sani, ya yi ikirarin cewa, duk da El-Rufai na da hannu a wajen hanashi tikitin takara a APC, hakan ba zai canja komai a siyasarsa ba

- Haka zalika, Sanatan ya ya ce akwai ranar da El-Rufai zai bar ofishin nasa, zai kuma yi bayani dalla dalla yadda ya gudanar da mulkin nasa

Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai, Shehu Sani, ya bayyana gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin wanda bai sanu a ko ina ba. Haka zalika, Sani, wanda ke takarar tazarcensa karkashin jam'iyyar PRP, ya ce babu tsiyar da gwamnan ya tsinanawa jihar.

Sanata Shehu Sani, ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PRP, kwanaki uku bayan da APC ta hana shi tikitin takara a jam'iyyar. Ya kuma zargi gwamnan jihar da kulla tuggun da ya sa jam'iyya mai mulkin ta hana shi tikitin takarar.

Da yake jawabi a shirin gidan talabijin na Arise TV a ranar Alhamis, Sani ya ce jam'iyyar PRP na ci gaba da zama barazana ga APC a jihar Kaduna, yana mai cewa, "wannan ne ma dalilin da ya sa a kowacce safiya da maraice, suna lalata fastoci da alluran yan takarar jam'iyyarmu. Suna cutar da mambobinmu. Idan da a ce mu ba barazana bane a garesu, da basu kula mu ba."

KARANTA WANNAN: Dalilin da yasa ya zama wajibi a jinjinawa shugaban kasa Buhari - Sanata Shehu Sani

Sanata Shehu Sani: Babu wani abun kirki da El-Rufai ya tsinanawa Kaduna
Sanata Shehu Sani: Babu wani abun kirki da El-Rufai ya tsinanawa Kaduna
Asali: UGC

Sani, ya yi ikirarin cewa, duk da El-Rufai na da hannu a wajen hanashi tikitin takara a APC, hakan ba zai canja komai a siyasarsa ba, inda ya kuma ce "shugaban kasa Buhari ya ziyarci Kaduna ba sau daya ba, amma ka taba jin ance yazo kaddamar da wani aikin da gwamnatin jihar tayi?"

Dan majalisar dattijan, ya bayyana cewa shi da El-Rufai ba sa ga maciji, saboda banbance banbancen da ke tsakaninsu na siyasa da kuma hangen nesa.

"Na shafe kusan gaba daya rayuwata ina kwatarwa jama'a 'yancin su. A lokacin mulkin soji, kusan shekaruna sun kare ne a gidan kurkuku. Ko daga nan zaka fahimci inda banbancin yake, amma shi me zainyi takama da shi.?

"Ai akwai ranar kin dillanci, akwai ranar da zai bar ofishin nasa, zai kuma yi bayani dalla dalla yadda ya gudanar da mulkin nasa," a cewar Sani.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel