Keke da keke: Ganduje ya kaddamar da bincike kan Kwankwaso

Keke da keke: Ganduje ya kaddamar da bincike kan Kwankwaso

A ranan Laraba, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kai karan tsohon gwamnan jihar kuma Sanata, Rabiu Musa Kwankwaso, hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin wato EFCC.

Ganduje ya kai karan tsohon maigidansa ne hukumar yaki da rashawan ne saboda ya karkatar da wasu makudan kudi da ya kamata a yi ayyukan gine-ginen hanya da su.

Kana, Ganduje ya bayyana cewa hukumar EFCC ta kaddamar da bincike kan yadda Kwankwaso ya karkatar da kudin gina hanya kilomita biyar a kananan hukumomin jihar Kano 44.

Gwamnan ya laburta wannan ne yayin rantsar da kwamitocin yakin neman zabe 12. Yace hukumar EFCC ta gano yadda gwamnatin jiya ta cire kudaden.

KU KARANTA: Tsohon shugaba PDP, Adamu Muazu ya koma APC

Yace: "Lokacin da nike mataimakin gwamna, an yarda cewa kananan hukumomi 44 zasu dauki nauyin kashi 90 ciki 100 na aikin, sannan gwamnatin jihar ya daukin nauyin kashi 10 da ya rage."

“Amma Kwankwaso ya kwace kashi 90 din daga hannun kananan hukumomin 44, ya biya yankwangila wasu yan sullala, sannan yayi amfani da sauran wajen yakin neman zaben shugaban kasansa."

"Yan kwankwasiyya sun fara ikirarin cewa su sukayi aikin kilomita biyar, amma zan fallasasu."

Amma lokacin da jaridar Daily Trust ta tuntubi kwamishanan ayyukan lokacin gwamnatin Kwankwaso, ya bayyana cewa zargin da Ganduje keyi karya ne kawai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: chttps://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel