Jeff Bezos, mai kudin duniya zai tsinke igiyar aure da Matar sa

Jeff Bezos, mai kudin duniya zai tsinke igiyar aure da Matar sa

Fitaccen attajirin nan na duniya da ya yiwa dukkanin bil Adama zarra da fintinkau ta fuskar uwar dukuma da tarin dukiya, Jeff Bezos, ya ce ya fara shirye-shiryen raba gari tare da sawwake wa matarsa, MacKenzie Bezos, bayan shekaru 25 na zaman aure.

Bezoan mai shekaru hamsin da hudu a duniya kuma wanda ya yiwa duk wani hamshakin attijira dukan koshi da wucin kece raini a bangaren tsagwaran dukiya, ya bayyana hakan ne a yau Laraba kwanaki uku gabanin cikar sa shekaru hamsin da biyar a duniya.

Sakon da fiyayyen attijirin ya zayyana tare da sa hannun mai dakin sa a shafin zauren sada zumunta na Twitter, sun bayyana amincewar su a kan wannan lamari da cewa ko da ba bu igiyar aure a tsakanin su za su ci gaba da kasancewa aminai kuma shakikan juna.

Jeff Bezos, mai kudin duniya zai katse igiyar aure da Matar sa

Jeff Bezos, mai kudin duniya zai katse igiyar aure da Matar sa
Source: UGC

Jeff Bezos tare da mai dakin sa, MacKenzie

Jeff Bezos tare da mai dakin sa, MacKenzie
Source: UGC

Jeff wanda shine mamallakin kamfanin hada-hadar kasuwancin kasa da kasa na Amazon, ya auri MacKenzie mai shekaru 48 tun a shekarar 1993 bayan kaunar juna ta mamaye zukatan su yayin haduwa a wurin aiki a shekarar 1991.

Mujallar fidda kididdiga ta duniya wato Forbes da kuma ma'adanar tarihi a yanar gizo ta Wikipedia, sun yi itifakin Bezos na da tarin dukiya ta Dalar Amurka Biliyan 137. Ma'aunin dukiyar sa a kamfanin Amazon ta kai kimanin dalar Amurka biliyan 160 bayan wasu sana'o'in daban musamman saye da sayarwa ta muhallai a kasar sa ta Amurka.

KARANTA KUMA: Kotu ta sanya ranar fara sauraron karar haramtawa shugaba Buhari takara a zaben 2019

Kasancewar dokokin da suka shafi aure musamman a nahiyyar Turai, masana da kuma masu sanya idanu sun tabbatar da cewa, wannan rabuwa ta Bezos da mai dakin sa za ta kasance mafi tsadar rabuwar aure a doron kasa.

Kafofin watsa labarai da dama na duniya sun ruwaito cewa, Bezos ya karbi ragamar attajiranci ta duniya a hannun mai kamfanin Microsoft, Bill Gates, bayan ya shafe tsawon shekaru 24 ya na rike da kambun na hamshakan ma su baiwa ta gidan rana na duniya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel