Soyayya? Sarkin Malaysia yayi murabus don ya auri sarauniyar kyan Rasha

Soyayya? Sarkin Malaysia yayi murabus don ya auri sarauniyar kyan Rasha

A karo na farko cikin tarihin kasar Malaysia, Sultan Muhammad na biyar a ranan Lahadi, ya kwance rawaninsa ya sauka daga sarautan kasar kuma ya auri sarauniyar kyau kamar yadda aka ruwaito.

Masarautar Malaysiya ta tabbatar da murabus dinsa ne bayan shekaru biyu akan mulki. Sarkin ya shahara da wasa da mota duk da yana mai shekaru 49.

Jawabin yace: "Mai martaba ya yi kira ga mutanen Malaysiya da su cigaba da hada kawunansu, su cigaba da hakuri da juna kuma su cigaba da aiki tare," Wan Ahmad Dahlan Abdul Aziz yace.

Masu zaban sarki a kasar zasu zauna kan wanda zai zama sarki.

Soyayya? Sarkin Malaysia yayi murabus don ya auri sarauniyar kyan Rasha

Soyayya? Sarkin Malaysia yayi murabus don ya auri sarauniyar kyan Rasha
Source: Facebook

Kasar Malaysiya ta kasance kasa wacce ake sauya sarki bayan kowani shekaru biyar tsakanin jihohi tara. Sun kasance suna hakan tun shekarar 1957.

Masarauta bata bayyana dalilin da ya sanya Sultan Mohammed na biyar yayi murabus ba amma an kasance ana hasashe wani abu tun lokacin da ya dau hutun jinya a watan Nuwambab 2018.

Rahotanno daga kafafen yada labaran Birtaniya da Rasha sun bayyana cewa sarkin ya auri wata tsohuwar sarauniyar kyan kasan Rasha a birnin Moscow.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel