Kuma dai: Atiku makiyin kabilar Fulani ne, kada wanda ya zabeshi - Miyetti Allah Kautal Horey ta yi kira ga mambobinta

Kuma dai: Atiku makiyin kabilar Fulani ne, kada wanda ya zabeshi - Miyetti Allah Kautal Horey ta yi kira ga mambobinta

Kungiyar Miyetti Allah Kautal Horey, wata gamayyar Fulani Makiyayan Najeriya ta yi kira ga yan Najeriya da kada a sake a zabi dan takaran shugabancin kasar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar.

Shugaban kungiyar ta kasa, Abdullahi Bodejo, ya bayyana hakan ne yayinda yake magana da manema labarai ranan Alhamis, 3 ga watan Junairu a birnin tarayya Abuja.

Bodejo ya ce Atiku makiyin kabilar Fulani ne kuma ya kamata a kwance rawanin Wazirin Adamawa da yake sanye dashi saboda bai cancanci matsayin ba.

KU KARANTA: Tsohon gwamnan jihar Kano, Hamza Abdullah, ya rasu

Yace: "Muna kira ga mai martaba Lamidon Adamawa da ya kwance rawanin Atiku Abubakar na wazirin Adamawa saboda bayanannan makiyin Fulani makiyaya ne kuma ya zagaye kansa da masu sukar kabilar Fulani kuma suna kira ga kashesu."

"Saboda haka, muna kira ga dukkan mambobinmu a fadin tarayya da kuma wasu kungiyoyin Fulani da suyi fito-na-fito da neman takaran Atiku Abubakar saboda bai kaunar makiyaya da Najeriya."

Kuma dai: Atiku makiyin kabilar Fulani ne, kada wanda ya zabeshi - Miyetti Allah Kautal Horey ta yi kira ga mambobinta

Kuma dai: Atiku makiyin kabilar Fulani ne, kada wanda ya zabeshi - Miyetti Allah Kautal Horey ta yi kira ga mambobinta
Source: Facebook

Ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya umurci jami'an tsaro da su sanya ainun basira kan Atiku saboda irin maganganun da yakeyi kan makiyaya

A makon da ya gabata, kungiyar Miyetti Allah MACBAN ya mara goyon bayanta ga shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel