Boko Haram: Gwamnatin tarayya za ta siya jiragen yaki 3 da N27bn a 2019

Boko Haram: Gwamnatin tarayya za ta siya jiragen yaki 3 da N27bn a 2019

- Gwamnatin tarayya na shirin kashe naira biliyan 27 a kasafin kudin 2019 wajen siyan jiragen yaki uku

- Ciki za a kuma siya kayayyakin agaji na rundunar sojinta da ke yaki da ta’addanci a yankunan kasar da dama

- Gwamnati ta ware makudan kudade ga hukumomin tsaro domin su samu damar magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta

Gwamnatin tarayya na shirin kashe naira biliyan 27 a kasafin kudin 2019 wajen siyan jiragen yaki uku da kuma kayayyakin agaji na rundunar sojinta da ke yaki da ta’addanci a yankunan kasar da dama.

A cewar jaridar Vanguard, cikakken bayanin kashe kudin na kunshe a cikin kasafin kudin 2019 wanda gwamnati ta saki a yan kwanakin da suka gabata.

Boko Haram: Gwamnatin tarayya za ta siya jiragen yaki 3 da N27bn a 2019

Boko Haram: Gwamnatin tarayya za ta siya jiragen yaki 3 da N27bn a 2019
Source: Facebook

A cewar takardar, gwamnatin tarayya na shirin siyan wani mota mai nuna alama da kudi naira miliyan 666.7 sannan ta ware wani kudin naira biliyan 1 don siyawa dakarun sojin kayan jigila.

Har ila yau, daga cikin kokarin da akee na yaki da ta’addanci a arewa maso gabas, an shirya naira miliyan 295 a gefe domin makarartar horo na musamman ga rundunar tsaro a Bunu Yadi, jihar Yobe.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa Hamza Abdullahi, tsohon gwamnan jihar Kano rasuwa a kasar Jamus

Baya ga na sojojin kasafin kudin ya nuna yadda aka ware kudade zuwa sassa daba-daban da kuma hukumomin gwamnati.

Don haka gwamnati ta ware makudan kudade ga hukumomin tsaro domin su samu damar magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta, yan makonni kadan kafin zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel