Yan kasuwa sun tafka mummunan asara a wata gobara da ta tashi a kasuwan Kaduna

Yan kasuwa sun tafka mummunan asara a wata gobara da ta tashi a kasuwan Kaduna

Yan kasuwa dake da shaguna a babbar kasuwar garin Kafanchan sun tafka mummunar asara bayan da wata gobara ta tashi a daren Litinin, 31 ga watan Disambar shekarar 2018, cikin karamar hukumar Jama’a ta jahar Kaduna.

Majiyar Legit.com ta ruwaito shaguna guda goma sha hudu ne suka kone kurmus, wanda ya janyo asarar naira miliyan daya da dubu dari biyar (N1,500,000), kamar yadda shugaban yan kasuwar, Alhaji Salisu Idris ya bayyana.

KU KARANTA; Kungiyar Musulman Najeriya ta koka kan kashe kashen da ake yi a Zamfara

Yan kasuwa sun tafka mummunan asara a wata gobara da ta tashi a kasuwan Kaduna

Gobara
Source: UGC

Shugaban kasuwar ya bayyana gobarar a matsayin wata jarrabi, inda yace ta girgiza yan kasuwar kwarai da gaske, kuma ta janyo musu mummunar asara, don haka yayi kira ga gwamnatin jaha data karamar hukuma dasu kai musu dauki.

Shima shugaban karamar hukumar Jama’a, Peter Danjuma ya jajanta ma yan kasuwar tare da bayyana alhininsa game da ibtila’in daya fada musu, sa’annan yayi alkawarin basu duk tallafin daya dace gwargwadon iko.

A wani labarin kuma, Akalla mutane Talatin ne suka gamu da ajalinsu a yayin da wata babbar motar daukan kaya watau Tirela ta tattakesu, daga cikinsu har da wata mata mai dauke da juna biyu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Litinin, 31 ga watan Disamba, ranar karshe ta shekarar 2018 da misalign karfe 11:45 na dare, kimanin mintuna 15 gabanin shiga sabuwar shekarar 2019 a awon bature kenan.

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar ma majiyarmu cewar mutanen su Talatin sun gamu da ajalinsu ne a daidai garin Gbagi tuntun dake kan babbar hanyar Ife zuwa Ibadan daga jahar Osun.

Sai dai ana zargin direban babbar motar da kasancewa a halin maye da marisa a daidai lokacin da yake tukin motar, ma’ana sai da ya bankadi barasa kafin ya fara tukin, wanda wannan hali ne da aka san direbobin Najeriya da shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel