Boko Haram: Sojin Najeriya sun soma kwashe jama'ar garin Baga zuwa tuddan mun tsira

Boko Haram: Sojin Najeriya sun soma kwashe jama'ar garin Baga zuwa tuddan mun tsira

Rundunar Sojojin Najeriya sun fara aikin kwashe mutanen garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa a jihar, zuwa tuddan mun tsira don tseratar da su daga yakin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin sojin Najeriyar da mayakan Boko Haram a yankin.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ ta fitar dauke da sa hannun mataimakin kakakin ta, Kanal Onyema Nwachukwu a ranar Lahadi, rundunar sojin Najeriyar ta ce matakin zai ba dakarunta damar yakar mayakan Boko Haram din a duk inda suke a garin.

Boko Haram: Sojin Najeriya sun soma kwashe jama'ar garin Baga zuwa tuddan mun tsira

Boko Haram: Sojin Najeriya sun soma kwashe jama'ar garin Baga zuwa tuddan mun tsira
Source: UGC

KU KARANTA: Sojojin ruwan Najeriya sun cafke wasu hatsabiban tsagerun Neja Delta

Legit.ng Hausa ta samu daga sanarwar cewa, matakin kwashe fararen hular bai shafi mazauna garuruwan da suka hada da Bama, Dikwa da kuma Mongunu ba, la’akari da cewa farmakin da dakarun Najeriyar za su kaddamar a Baga ba zai shafe su ba.

Wakilin majiyar mu da ke Maiduguri, ya tabbatar mana cewa wani lokaci da yammacin wannan Litinin, ake sa ran samun karin bayani kan shirin na kwashe fararen hular daga Baga, bayan kammala taron majalisar tsaro tsakanin kwamandojin rundunar ‘Operation Lafiya Dole’, sauran hukumomin tsaro da kuma gwamnatin jihar Borno.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a tsakiyar makon da ya gabata ne wasu gungun mayakan Boko Haram suka kai farmaki kan sansanin sojoji da ke Baga, wanda bayan shafe sa’o’i ana fafatawa, dakarun suka janye domin baiwa jiragen yaki damar gaggauta murkushe harin mayakan, sai dai rahotanni na nuni da cewa har yanzu mayakan suna garin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel