Abun tausayi: Karin bayani kan labarin 'yan agajin da aka sace a Sokoto

Abun tausayi: Karin bayani kan labarin 'yan agajin da aka sace a Sokoto

A ranar lahadin da ya gabata ne masu garkuwa da mutane sukayi awun gaba da 'yan Agaji 20 wadanda suke dawowa daga taron atisayi da suka gabatar a jihar Kebbi karkashin kungiyar Izalar Jos.

'Yan Agajin dai guda ashirin sun gamu da masu garkuwa da mutanen ne a kan hanyar su ta dawowa daga jihar Kebbi, inda suka gudanar da taron atisaye (camping) wanda majalisar agaji ta kasa ta kungiyar ta shirya.

Abun tausayi: Karin bayani kan labarin 'yan agajin da aka sace a Sokoto

Abun tausayi: Karin bayani kan labarin 'yan agajin da aka sace a Sokoto
Source: Facebook

KU KARANTA: Maganganu 7 daBuhari yayi a Uyo

Amma kamar yadda muka samu, da suka doshi dajin Gurbin Baure dake hanyan Jibiya ta jihar Katsina sai suka ci karo da masu garkuwa da mutane. 'Yan ggajin dai su kimanin 20 dukkanin su 'yan karamar hukumar Isa ne na jihar Sokoto.

Legit.ng Hausa ta samu cewa har yanzu dai suna hannun masu garkuwa da mutane. Sai dai wata majiyar ta tabbatar mana da cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi a basu kudin fansa Naira miliyan talatin (N30m).

A bangare guda kuma a dai-dai lokacin da jagororin kungiyar ta Izala suke ta kokarin hada kudaden da masu garkuwar suka bukata, wasu majiyoyin sun ruwaito cewa 'yan garkuwa da mutanen suna amfani da kayan agajin wadanda suka yi garkuwa da su wajen aiwatar da ayyukan su.

Sheikh Yusuf Sambo, mataimakin shugaban majalisar malamai na kungiyar ya nuna damuwar sa dangane da yanda ayyukan ta'ddanci da rashin tsaro suka yi kamari a kasar nan.

Yace wajibi ne gwamnati ta dau matakin gaggawa don ganin fitintinun rashin zaman lafiya da rashin tsaro sun zo karshe a Nijeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel