Duniya juyi-juyi: Yadda Dasuki ya taimaka wa Shugaba Buhari ya zama shugaban kasa a 1983

Duniya juyi-juyi: Yadda Dasuki ya taimaka wa Shugaba Buhari ya zama shugaban kasa a 1983

Sabanin yadda ake yadawa a wurare da yawa cewa tsohon mai baiwa Shugaba Jonathan shawara akan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasukin yana cikin Sojojin da suka je suka kamo Shugaba Buhari a juyin mulkin 1985, gamasasshen bayani ya nuna cewa ba haka bane.

Kamar dai yadda muka samu daga wasu majiyoyin da dama, Kanal Dasuki din a maimakon hakan ma kusan a iya cewa shine ya jagoranci aiwatar da juyin mulkin shekarar 1983 da Shugaba Buharin ya ci gajiyar sa ya zama shugaban kasa a wancen lokacin.

Duniya juyi-juyi: Yadda Dasuki ya taimaka wa Shugaba Buhari ya zama shugaban kasa a 1983

Duniya juyi-juyi: Yadda Dasuki ya taimaka wa Shugaba Buhari ya zama shugaban kasa a 1983
Source: Getty Images

KU KARANTA: Tsagerun Neja Delta sun yi barazanar hargitsa kasa a yayin zaben 2019

Legit.ng Hausa ta samu cewa tsohon dogarin Janar Muhammadu Buhari, lokacin da ya Shugabanci kasarnan a mulkin Soja, Mustapha Jokolo, ya bayyana irin rawar da Kanal Dasuki ya taka wajen samun nasarar juyin mulkin da Sojoji suka yi a shekarar ta 1983.

Mustapha Jokolo dai ya yi wadannan bayanan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da wata jarida, a martanin da yake mayar wa kan wani littafi da Sarkin da ya gaje shi a Sarautar ta Gwandu, Janar Muhammadu Iliyasu Bashar mai ritaya, ya rubuta.

A cewar tsohon Sarkin Jokolo, Dasukin ya taka mahimmiyar rawa ta hanyar daukan nauyin juyin mulkin da kudin sa da kuma kitsa yadda juyin mulkin wanda a cikin sa ne Muhammadu Buhari ya zama Shugaban kasa, zai yi nasara a 1983.

Da yake magana kan wasu bayanai da ke cikin littafin na Janar Bashar, Jokolo, ya nanata maganan na shi inda yake cewa, “A bisa zahirin gaskiya, wannan shi ya sanya nakan ji zafi sosai kan halin da Dasukin yake ciki a halin yanzun. Na damu sosai da hakan.

“Wannan gaskiyan kenan. Baccin na kawo Dasuki, cikin lamarin juyin mulkin ba, na 1983, da juyin mulkin da Buharin ya zama shugaban kasa a cikin sa bai yi nasara ba. Sambo Dasuki ne ya shirya mani komai na yadda za a yi juyin mulkin. Ni shawarar juyin mulkin ne kawai na ba shi.

“Na rantse da Allah. Duk shi ne ya taro mutanan da aka yi juyin mulkin da su. Duk shi ya tsara komai. Ya taka rawa a juyin mulkin sosai, a zahirin gaskiya….Sai na hada su da Sambo Dasukin, sai…kai ko a lokacin da muke shirya yanda juyin mulkin da Buharin ya zama shugaban kasa a cikin sa, zai gudana, Sambo Dasukin ne yake nemo mana kudaden da za a yi komai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel