Kunne-ya-girmi-kaka: Yadda aka sa Buhari cikin mari yayin juyin mulkin da aka yi masa a 1985

Kunne-ya-girmi-kaka: Yadda aka sa Buhari cikin mari yayin juyin mulkin da aka yi masa a 1985

Sabanin yadda ake yadawa a wurare da yawa cewa tsohon mai baiwa Shugaba Jonathan shawara akan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasukin yana cikin Sojojin da suka je suka kamo Shugaba Buhari a juyin mulkin 1985, gamasasshen bayani ya nuna cewa ba haka bane.

Kamar dai yadda muka samu daga wasu majiyoyin da dama, Kanal Dasuki din a maimakon hakan ma kusan a iya cewa shine ya jagoranci aiwatar da juyin mulkin shekarar 1983 da Shugaba Buharin ya ci gajiyar sa ya zama shugaban kasa a wancen lokacin.

Kunne-ya-girmi-kaka: Yadda aka sa Buhari cikin mari yayin juyin mulkin da aka yi masa a 1985
Kunne-ya-girmi-kaka: Yadda aka sa Buhari cikin mari yayin juyin mulkin da aka yi masa a 1985
Asali: UGC

KU KARANTA: An gano sabbin illolin shan shisha

Legit.ng Hausa ta tsinkayi Kanal Abdulmumini Aminu mai ritaya, wanda dan asalin Jihar Katsina ne, ya bayyana ko su waye Manjo-Manjo din guda uku da ya jagoranta wajen kamo Shugaba Buhari a 1985 lokacin da Janar Babangida yayi masa juyin mulki, a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a cikin jaridar ‘Sunday Trust,’ ta watan Agusta 2015.

Abdulmumini Aminu, ya ce, mutane uku ne wadanda shi da kansa ya jagorance su, suka je suka kamo Shugaban kasan na wancan lokacin, (Janar Muhammadu Buhari), sauran biyun sune, Lawan Gwadabe da kuma John Madaki.

Ya ce, “Tilas na bayar da shaidar ni na jagoranci kamo shi. Na ta fi Barikin Dodon Barrack a lokacin, tare da rakiyar Sojoji biyu, Manjo John Madaki da kuma Lawan Gwadabe. Mu uku ne muka je, amma a zahiri, ni na hau sama na kamo Buharin.

“Na kamo shi da cikakkiyar girmamawa, na sha karantawa a cikin kafafen yada labarai, mutane na cewa, wai mun ci mutuncin sa, mun wulakanta shi. Sam hakan ba gaskiya ne ba. Ni da Janar Buharin ne kadai muka san hakikanin abin da ya gudana a tsakaninmu a saman benen, ba wani abu makamancin hakan da ya faru.

“Mun ba shi duk girmamawar da ya kamace shi a matsayin sa na babba gare mu, domin ai ko kafin wannan lokacin, muna ba shi cikakkiyar girmamawa, saboda irin halin sa. Har kawo yau, muna ganin kimarsa, babu kuma wani munafunci a tsakanin mu da shi, shi kuma ya san matsayin bin umurni a aikin Soja, a lokacin da duk na gaba da kai ya sanya ka yin wani aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel