Sarkin Tsafe ya bayar da umarnin cafko wadanda suka yi zanga-zanga a Zamfara

Sarkin Tsafe ya bayar da umarnin cafko wadanda suka yi zanga-zanga a Zamfara

Sarkin Tsafe, Muhammad Bawa, ya bawa dukkan hakiman masarautar sa umarnin zakulo dukkan wadanda suka gudanar da zanga-zangar da aka yi a Zamfara, jiya, Litinin.

Sarkin ya bayyana haka ne a yau, Talata, yayin karbar bakuncin kwamishinan 'yan sanda na jihar Zamfara, Usman Belel, a ziyarar da ya kai domin bawa jama'ar masarautar tabbacin basu kariya.

"Ban taba taba fuskntar wata zanga-zanga daga matasan wannan masarauta ba sai wannan karon, hakan ya nuna cewar sun dade suna tsara hakan, musamman idan aka yi la'akari da yadda suka fito lokaci guda suka rushe sakatariyar karamar hukuma," a jawabin Sarkin.

Bawa ya kara da cewa tare babbar hanyar garin Tsafe zuwa kauyen Kucheri da masu zanga-zangar suka yi ne yafi damunsa.

Sarkin Tsafe ya bayar da umarnin cafko wadanda suka yi zanga-zanga a Zamfara

zanga-zanga a Zamfara
Source: Twitter

Sannan ya ce tuni ya bawa dukkan hakimansa umarnin su bankado wadanda suka yi zanga-zangar domin a yi masu hukuncin da zai zama darasi ga masu son yin irin wannan hali a nan gaba.

A nasa jawabin, kwamishinan 'yan sanda, Usman Belel, ya shaidawa Sarkin cewar al'amura yanzu sun koma daidai kuma tuni jami'an 'yan sanda sun fara binciken abinda ya haddasa zanga-zangar.

DUBA WANNAN: Tsibbu: Mun daina saka dan kamfai - Matan wata jami'ar Najeriya

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa shugaban rundunar sojin sama ta kasa, Air Marshal Abubakar Baba Sadique, umarnin gaggauta zuwa jihohin Sokoto da Zamfara a yau, Talata, da gobe, Laraba, domin yin kiyasin ta'adin da 'yan ta'adda suka yi a sassan jihohin.

A jawabin da Garba Shehu, kakakin shugaba Buhari, ya fitar, ya ce shugaban rundunar sojin saman zai shafe tsawon kwanaki biyu na hutun bikin Kirsimeti a jihohin.

An kashe dubban mutane a cikin shekaru biyu sakamakon aiyukan 'yan ta'adda a kauyukan jihar Zamfara.

Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da kisan mutane a Birnin Magaji dake karamar hukumar Tsafe da garin Magami dake masarautar Faru a karamar hukumar Maradun da 'yan ta'adda suka yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel