Gaskiyar magana: Yan siyasa ne ke rura wutar rikicin makiyaya da manoma - Miyetti Allah

Gaskiyar magana: Yan siyasa ne ke rura wutar rikicin makiyaya da manoma - Miyetti Allah

- Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, ta zargi 'yaan siyar kasar da zama sanadin rura wutar rikicin da ke faruwa tsakain makiya da manoma a wasu sassa na kasar

- Kungiyar ta ce 'yan siyasar na afani da wannan rikici don cimma wata bukata tasu musamman na hana jituwa tsakanin Fulani da sauran kabilu

- Kungiyar ta kuma zargi gwamnatoci a matakai daban daban da nuna wariya ga Fulani, ta hanyar mayar da su saniyar ware a harkokin mulkin gwamnatin

Shugaban kungiyar Fulani da aka fi sani da Miyetti Allah, Alhaji Bello Abdullahi Bodejo, ya ce 'yan siyasa ne ke rura wutar rikice rikicen da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma a wasu sassa na fadin kasar.

Bodejo ya bayyana hakan a Sokoto, a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a ranar Talata. Ya yi nuni da cewa rashin jituwar da ake samu tsakanin makiya da manoma wanda yaki ci yaki ciyewa, na faruwa ne sakamakon gaza bin hanyoyin da suka dace a gargajiyance.

A cewar Bodejo: "Sai dai ba kamar yadda aka saba yin rikici a warwares hi ba, wannan rikicin na makiya da manoma na samun tagomashi a wajen 'yan siyasa, suna amfani da rikicin wajen cimma wata manufa tasu ta kawo sabani tsakanin kabilar Fulani da sauran kabilu.

KARANTA WANNAN: Buhari ya ki rattaba hannu kan kudirin sabunta dokar hukumar NBC, ya bayyana daili

Gaskiya magana: Yan siyasa ne ke rura wutar rikicin makiyaya da manoma - Miyetti Allah
Gaskiya magana: Yan siyasa ne ke rura wutar rikicin makiyaya da manoma - Miyetti Allah
Asali: Depositphotos

"Da zaran anyi hatsari ko an yi wani rikici, zakaga wani ya dauki hotuna ya tura a kafofin sadarwa na zamani, ya ce Fulani ne suka aikata wannan kisan," a cewar Bodeje.

Ya jaddada cewa makiyaya na kwarai ba sa daukar makamai ko wanne iri wajen yi kiwo, face sanduna da suke amfani da su wajen karkatar da akalar dabbobinsu, kuma an sansu da hakan tun zamanin dauri.

Shugaban miyetti Allah sai ya ga laifin gamnati a matakai daban daban na mayar da a'ummar Fulani saniyar ware a cikin harkokin gudanar da mukin gwamnatin, tare da cewar mafi yawan dokar hana kiwo a sarari da wasu gwamnatocin jihohin kasar suka kakaba ya sabawa wasu dokokin 'yan cin zaman dan kasa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel