Dandalin Kannywood: 'Auren' Jaruma Maryam Booth da Sadiq Zazzabi ya bar baya da kura

Dandalin Kannywood: 'Auren' Jaruma Maryam Booth da Sadiq Zazzabi ya bar baya da kura

Irin ce-ce-ku-ce da surutan da ake ta faman yi a tsakanin ma'abota kafofin sadarwar zamani musamman ma masu sha'awar kallon fina-finan Hausa kan wasu hotuna da fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Maryam Booth ta wallafa na bikin aure a iya cewa ya bar baya da kura.

Jarumar dai ta wallafa hotunan ta tare da Sadiq Zazzabi mawakin Hausa a cikin wata shiga irin ta ango da amarya, hotunan da ke nuna kauna da soyayya tsantsa tamkar da gaske.

Dandalin Kannywood: 'Auren' Jaruma Maryam Booth da Sadiq Zazzabi ya bar baya da kura
Dandalin Kannywood: 'Auren' Jaruma Maryam Booth da Sadiq Zazzabi ya bar baya da kura
Asali: Facebook

KU KARANTA: Nafisa Abdullahi ta bayyana matsayin Ali Nuhu a wurin ta

Hotunan sun ja hankalin mabiyanta da ma'abota fina-finan Hausa sosai inda akayi ta yada hutunan a shafukan sada zumunta na intanet cewa Maryam Booth za ta yi aure.

Legit.ng Hausa ta samu cewa yayin da wasu ke tunanin a fim ne, wasu kuwa cewa sukeyi da gaske ne za ta auri Sadiq Zazzabi ganin cewa mawaki ne da ba ya fitowa a fim.

Sai dai binciken majiyar mu da ta tuntubi Maryam Booth domin tabbatar da ko da gaske ne za ta auri Sadiq Zazzabi ya tabbatar da cewa shirin fim ne kawai ba da gaske bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng