EFCC ta kai mamaya gidan ýaýan Atiku a Abuja

EFCC ta kai mamaya gidan ýaýan Atiku a Abuja

- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun kai mamaya gidan da ýaýan Atiku Abubakar biyu ke zama a Abuja a karshen mako

- Yayainda yayan Atiku ba sa gari an tattaro cewa an kama dan Orji tare da dan uwansa inda aka tafi da su ofshin EFCC

- Wani kakakin EFCC yace baida masaniya akan mamayar, amma ya nuna kokwantoi cewa an kai mamaya gidan ýaýan Atiku

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun kai mamaya gidan da ýaýan Atiku Abubakar biyu ke zama a Abuja a karshen mako, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Haka zalika Chimeka Orji, dan tsohon gwamnan jihar Abia, Theodore Orji na zama ne a gidan. An kuma rahoto cewa jami’an hukumar yaki da rashawan sun binciki sashinsa.

Koda dai majiyoyi sun bayyana cewa gidan ýaýan Atiku ne musababbin zuwansu, wani kakakin hukumar yaki da rashawar ya bayyana cewa babu mamaki saoda Chiemeka suka kai mamayar.

Mamayar da aka kai gidan Aliyu Da Mustapha Atiku Abubakar a Maitama a ranar Asabar na zuwa ne kwana guda bayan hukumomin tarayya sun daskarar da asusun abokin takarar Atiku, Peter Obi. Hukumomin yaki da rasha biyu EFCC da ICPC sun karyata daskarar da asusun bankin Obi.

Paul Ibe, kakakin iyalan Atiku Abubakar, ya tabbatar da binciken a ranar Lahadi, cewa jami’an da suka gudanar da “lamarin mai cike da barazana basu samu komai ba.

Daga Aliyu har Mustapha ba su gari a lokacin da hukumar yaki da rashawar suka iso domin dukkaninsu biyu na karatun digiri na biyu a jami’o’in kasashen waje, amma an tattaro cewa an tafi da wadanda ke zama da su a gidan ofishin EFCC tare da wasu kayayyakinsu, cewar majiyoyi.

EFCC sun kai mamaya gidan ýaýan Atiku a Abuja
EFCC sun kai mamaya gidan ýaýan Atiku a Abuja
Asali: UGC

Daga cikin wadanda aka kama harda Chiemeka wanda mahaifinsa ya kasance sanata mai ci kuma wanda ke fuskantar binciken rashawa a yanzu haka a hukumar EFCC.

An tattaro cewa an kai Chiemeka ofishin EFCC da ke Abuja tare da dan uwansa, da motoci biyu da aka gani tare da su.

KU KARANTA KUMA: Hadiman yan majalisa sun aika wasika ga Buhari da EFCC kan alawus dinsu, sun zargi Saraki da Dogara da karkatar da kudi

Majiyoyi sun bayyana cewa an saki Chiemeka da dan uwansa bayan amsa wasu tambayoyi a ofishin EFCC, amma har yanzu motocinsu guda biyu na hannun hukumar a safiyar ranar Litinin.

Ba’a samu jin tab akin Chiemeka a, domin lamban wayarsa sun ki shiga. Haka zalika ba’a ji daga yayan Atiku ba.

Wani kakakin EFCC yace baida masaniya akan mamayar, amma ya nuna kokwanto cewa an kai mamaya gidan ýaýan Atiku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel