Kasar Saudiyya ta bayar da tallafin buhunan abinci 140,468 ga Najeriya

Kasar Saudiyya ta bayar da tallafin buhunan abinci 140,468 ga Najeriya

Masarautar Saudiyya ta hannun cibiyar bayar da tallafi na Sarki Salman ta bayar da tallafin buhuhunan abinci ga yan gudun hijiran da harin Boko Haram ya cika da su a jihohin Borno da Yobe.

Da yake jawabi a wajen rabon kayyakin sansanin kauyen Teacher, Maiduguri, jihar Borno, darakta janar na hukumar bayar da agajin gaggawa na kasa, Injiniya Mustapha Maihaja ya bayyana cewa za’a raba Kwando 125,317 na kayayyakin abincin ga gidae 33,343 a sansanoni da al’umman jihar Borno na tsawon watanni hudu masu zuwa.

Kasar Saudiyya ta bayar da tallafin buhunan abinci 140,468 ga Najeriya
Kasar Saudiyya ta bayar da tallafin buhunan abinci 140,468 ga Najeriya
Asali: Depositphotos

Maihaja ya yabama kokarin ministan tsaro ritaya birgediya janar Mansur Dan Ali wanda ya taimaka da abinci a yankin arewa maso gabas.

KU KARANTA KUMA: Zanga-zangan majalisar dokoki: Majalisar wakilai ta aika sammaci ga ministar kudi

A borno ana rabon buhuhunan shinkafa da wake girman 25kg guda 125,372 da kuma kwalayen kayan dandanon abinci 62,686 kai tsaye da taimakon hukumomin NEMA, SEMA da kuma masu ruwa da tsaki.

Kakakin NEMA, Sani Datti yayi bayanin cewa a kowani gida mai dauke da mutane shida za su samu kwandon abinci na 59.8kg na tsawon wata guda.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Anyi gagarumin sauyi a hukumar sojin Najeriya, sabbin jami’ai za su yi yaki da ta’addanci a arewa maso gabas

Shugaban tawagar, mataimakin darakta na hukumar agaji daga cibiyar tallafi na sarki Salman, Naseer Alsubaie yace tallafin zai amfani yan gudun hijira sama da 840,000 a yankin arewa maso gabas.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel