Yanzu-yanzu: An kaddamar da nadin sarautan Atiku a matsayin Wazirin Adamawa

Yanzu-yanzu: An kaddamar da nadin sarautan Atiku a matsayin Wazirin Adamawa

An kaddamar da bikin nadin sarautan dan takaran kujeran shugaban kasan jam’iyyar adawa Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin Wazirin Adamawa na bakwai a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Tsaffin gwamnoni, sarakunan gargajiya, malaman addini, da sauran manyan baki daga sassan Najeriya suna hallare a taron.

Yanzu-yanzu: An kaddamar da nadin sarautan Atiku a matsayin Wazirin Adamawa
Yanzu-yanzu: An kaddamar da nadin sarautan Atiku a matsayin Wazirin Adamawa
Asali: Facebook

Daga cikin wadanda suka halarta sune tsohon gwamnan jihar Adamawa, Bala Ngillari; Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tawagar yan Kwankwasiyya, Wakilin gwamnan jihar Cross Riba, Ben Ayade, wakilin gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom.

Abokin tafiyar Atiku a takaran shugaban kasa kuma gwamnan jihar Anambara, Peter Obi; tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; tsohuwar ministar harkokin mata, Asiha Jummai Alhassan.

Yanzu-yanzu: An kaddamar da nadin sarautan Atiku a matsayin Wazirin Adamawa
Yanzu-yanzu: An kaddamar da nadin sarautan Atiku a matsayin Wazirin Adamawa
Asali: Twitter

Wajen taron na zagaye da hotunan jam’iyyar PDP yayinda makada da masu busan fadar Lamidon Adamawa suke nishadantar da mutane.

Yanzu-yanzu: An kaddamar da nadin sarautan Atiku a matsayin Wazirin Adamawa
Yanzu-yanzu: An kaddamar da nadin sarautan Atiku a matsayin Wazirin Adamawa
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng