Tsintuwa ba sata ba: Wani dan baiwa ya tsinci Naira biliyan 2 cikin wata dilar gwanjo
Hausawa dai na cewa tsintuwa ba sata ba, idan mai abu ya gani a bashi abun shi. Haka nan wasu kuma na cewa idan Allah ya soka da arziki to tsintuwa yake sawa kayi kamar daga sama.
To wannan ma dai labarin kusan a iya cewa haka ne domin kuwa wani ne Allah yayi wa gam-da-katar bayan da ya tsinci dame a kala lokacin da ya siya wata taskira ta adana muhimman abubuwa akan Naira 182,000 amma sai ya tsinci Naira biliyan 2.

Asali: Instagram
KU KARANTA: An kama 'yan luwadi 2 a garin Kano
Legit.ng Hausa ta samu cewa wani sanannen mai gabatar da shire-shire a wani gidan Talabijin din kasar Birtaniya da kuma yake sayar da gwanjo, Dan Dotson ne ya bayar da wannan labarin a cikin shirin nasa da yake gabatarwa.
Sai dai da fadin hakan, sai kau akayi sa'a wadanda suka sayar da ma'ajiyar tun asali suka ji labari inda suma suka tada balli kan cewa lallai-lallai sai dai a tada ciniki ko kuma dan basu wani kaso a cikin kudin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng