Jagwalgwalo: Wani matashi ya guji matar sa, ya aure mahaifiyar ta
Mun samu labarin wani lamari dake kama da almara inda wani matashi mai shekaru ashirin da biyu mai suna Mahto Suraj, ya gujewa matasa da suka dade a tare mai suna Latila sannan kuma ya auri mahaifiyar ta mai suna Asha Devi, mai shekaru araba’in da biyu.
Wani abin al’ajabi ya faru ne a lokacin da mahaifiyar matar ta kai masu ziyara, kamar yadda jaridar India Times, ta ruwaito Asha ta bar mijinta mai aiki a wata masana’anta a Delhi, ta auri mijin ‘yarta inda suka yi aure irin na gargajiya, da kuma na kotu.

Asali: Getty Images
KU KARANTA: Lauyan Sule Lamido ya koma PDP
Legit.ng Hausa ta samu cewa amma a yanzu Suraj, na neman a raba auransa da mahaifiyar matan saboda ya koma da tsohonwar matarsa Latila.
A wani labarin kuma, Wani malamin addinin kirista daga cikin daliban babban malamin addinin na kirista Emmanuel Badu Kobi dake shugabantar rukunin majami'un Glorious Wave Chapel International watau Fasto Osofo an kama shi turmi da tabarya da wata matar aure.
A wani faifan bidiyon da yayi ta yawo a kafafen sadarwar zamani da yanar gizo, an ga Faston karara yana fasikanci da matar auren wanda hakan ya haifar da zazzafar muhawara da cece-kuce a tsakanin mabiyan addinin na kirista.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng