Kaso 70 cikin 100 na wadanda zan yi aiki da idan na doke Buhari matasa ne da mata – Atiku

Kaso 70 cikin 100 na wadanda zan yi aiki da idan na doke Buhari matasa ne da mata – Atiku

- Dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa matasa da mata ne za su fi yawa a gwamnatinsa idan har ya lashe zabe

- A cewarsa kaso 40 za su kasance matasa sannan 30 kuma mata

- Ya bukaci masoyansa da su tabbatar sun fito a ranar zabe domin kada kuri'a

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar ya bayyana wa tarin matasa da suka kai masa ziyara a garin Yola, babbar birnin jihar Adamawa cewa kada su ji koma idan har ya kayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa, lallai matasa da mata ne za su fi yawa a gwamnatin sa.

A cewarsa, akalla matasa da mata ne za su kwashe kaso 70 na nade-naden da zai yi.

Matasan dai sun ziyarce shi domin jadadda goyon bayan su a gare shi a zaben 2019 mai zuwa.

Kaso 70 cikin 100 na wadanda zan yi aiki da idan na doke Buhari matasa ne da mata – Atiku
Kaso 70 cikin 100 na wadanda zan yi aiki da idan na doke Buhari matasa ne da mata – Atiku
Asali: Facebook

“Kaso 40 bisa 100 matasa zan nada, sannan kaso 30 bisa 100 zan nada mata ne. Allah ya riga yayi mini gyadar dogo domin tabarkalla kam. Amma kune nake tausaya wa. Idan baku fito kun zabi PDP ba to karshen ta haka zaku ci gaba da zama cikin kunci da wahala.

KU KARANTA KUMA: An fi sata sosai a karkashin gwamnatin Buhari - PDP

”Ku tabbata ranar zabe kun fito kun yi zabe kuma ku kasa, ku tsare sannan ku raka.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng