Allah daya gari bamban: Yadda wani mahaifi ya yanka diyarsa don shayar da dodonsa jini
Shugabar karamar hukumar Konshisha, Mrs Justina Ubebe, ta tabbatar da kisan wata yarinya karama, wacce mahaifinta, John Depuun ya yankata, a matsayin sadaukarwa ga dodon kauyensu na Tse-Agberagba da ke karamar hukumar.
Da take tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai ta wayar tarho a ranar Alhamis, a Makurdi, Ubebe ta bayyana wannan lamari a matsayin "al'abi da kuma rikitarwa."
KARANTA WANNAN: Yadda Buhari yake lashe zabe a yanar gizo haka zai lallasa Atiku a zaben zahiri - PMBCN

Asali: Depositphotos
Ta ce, kisan gillar da ya faru a ranar Laraba, tuni aka sanar da jami'an rundunar 'yan sanda, kuma har an cafke wanda ake zargin.
Haka zalika, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Moses Yamu, ya ce an cafke mahaifin yarinyar tare da fara gudanar da bincike a kansa.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng