Hukumar EFCC tayi babban kamu a tsakanin ma'aikatan hukumar INEC
Hukumar nan ta gwamnatin dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta gurfanar da wasu manyan jami'an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC su 22 a gaban kotu bisa zargin laifin almundahana.
Kamar yadda muka samu, jami'an EFCC din sun kai ma'aikatan INEC din ne su 22 da kuma daraktan kudi na ofishin hukumar a jihar Kogi a gaban wata babbar kotun jihar dake zaman ta a garin Lokoja.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Fada ya kacame tsakanin dattawan Inyamurai kan Buhari
Legit.ng ta samu cewa EFCC din dai tana tuhumar jami'an nan da laifin karbar na goro har Naira miliyan 32 lokacin zaben 2015 wajen aikata ba daidai ba.
A wani labarin kuma, Dan takarar Sanata a Kano ta tsakiya a jam'iyyar APC, tsohon gwamnan Kano Mallam Ibrahim Shekarau ya ce "babu tantama shugaban kasa Muhammadu Buhari zai koma kan kujerarsa a zaben 2019 da izinin Allah.
Mallam Shekarau ya ce zaben da za a yi a badi 2019 ba irin na 2015 bane. Musulmi da Musulmi ne kuma dan arewa ne da dan arewa a tsakanin APC da PDP. Don haka Buhari zai kada Atiku amma ba da irin rinjayen wancan yanayin ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng