Cin mutunci: Yadda ministan Buhari ya tozarta wani Sanata a gaban matar sa

Cin mutunci: Yadda ministan Buhari ya tozarta wani Sanata a gaban matar sa

Rikicin cikin gida na jam'iyyar APC a jihar Ribas bai kama hanyar zuwa karshe ba bayan da Sanata a jihar dake wakiltar mazabar shiyyar kudu maso gabashin jihar, Sanata Magnus Abe ya zargi ministan sufuri da tozarta shi a gaban matar sa.

Sanatan dai ya yi wannan ikirarin ne a cikin wata fira da yayi da mujallar Interviewmagazine a 'yan kwanakin da suka shuge lokacin da yake karin haske akan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar tasu a jihar.

Cin mutunci: Yadda ministan Buhari ya tozarta wani Sanata a gaban matar sa
Cin mutunci: Yadda ministan Buhari ya tozarta wani Sanata a gaban matar sa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Tsohon jami'in Birtaniya ya caccaki Buhari

Legit.ng Hausa ta samu cewa Mista Abe ya ce ministan na sufuri ya je ne har gidan sa kuma a gaban matar sa ya fada masa cewa mai kar ya kuskura yayi takara a zaben 2019 wanda shi kuma yake ganin hakan babban tozarci ne ga dukkan dan siyasa.

A wani labarin Dan takarar kujerar shugabcin kasar Najeriya a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya bayar da tallafin karatu kyauta ga iyalan sojojin da harin ta'addacin Boko Haram ya salwantar da rayuwar su barikin sojin Metele, jihar Borno.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar dauke da sa hannun sa a ranar Larabar da ta gabata a ofishin yakin neman zaben sa dake a garin Abuja, babban birnin tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng