Rikicin makiyaya da manoma ya yi silar mutuwar mutane da dama a Katsina
- Sabon karan batta tsakanin makiyaya da manoma a kauyen Gora da ke jihar Katsina ya zama silar salwantar rayukan mutane da dama
- Rikicin ya barke ne biyo bayan yadda wani makiyaya ya tura dabbobinsa cikin gonar wani manomi da ke girbin wakensa
- Sai dai, rundunar 'yan sanda ta ce ta yi kokarin kwantar da tarzomar
Sabon karan batta tsakanin makiyaya da manoma a kauyen Gora da ke jihar Katsina ya zama silar salwantar rayukan mutane da dama, kamar dai yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito.
"Rikicin ya barke ne biyo bayan yadda wani makiyaya ya tura dabbobinsa cikin gonar wani manomi da ke girbin wakensa," mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta jihar Katsina, Isah Gambo ya shaidawa NAN.
Wata majiya ta shaidawa NAN cewa rikicin ya barke ne da yamma likis a ranar Talata, inda akai zargin cewa nan take makiyayin ya kashe manomin.
Majiyar ta kuma zargi cewa iyalan manomjn da aka kashe, suma suka taru suka kashe makiyayin.
KARANTA WANNAN: Sauya sunayen 'yan takara: APC a Niger sun fusata, sun sha alwashin daukar mataki

Asali: Depositphotos
A cewar majiyar, a lokacin da iyalan makiyayin suka ji labarin cewa an kashe masu dan uwa, suma sai suka yi tasaga suka dira garin Gora, inda ba wata wata suka fara harbin duk wani manomi da suka ci karo da shi.
Akalla mutane 12 ne ake tunanin sun mutu, yayin da tara suka samu raunuka a wannan rikicin da ya barke a kauyen Gora, da ke cikin karamar hukumar Safana, jihar Katsina.
Sai dai, rundunar 'yan sanda ta ce ta yi kokarin kwantar da tarzomar.
Mr Gambo ya shaidawa manema labarai a ranar Laraba a Katsina cewa, tuni rundunar 'yan sanda ta tura jami'anta na MPF zuwa yankin da lamarin ya shafa, don tabbatar da ganin an maido da zaman lafiya a yankin.
Rikici tsakanin makiyaya da manoma ya lakume rayukan dubunnan mutane a jihohi da dama na Nigeria da suka hada da Benue, Taraba, Kaduna da Filato.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng