Zaben fidda gwani: APC ta yi barazanar daukar mataki kan wadanda ba su janye kara a kotu ba
Jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki ta caccaki mambobin ta da suka shigar da kara kotu don neman hakkin su bayan gudanar da zabukan fidda gwani na jam’iyyar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da rigingimu a kotuna da dama a fadin kasar nan suka dabaibaye jam’iyyar saboda yadda ta gudanar da zabukan fidda gwaninta.
Yan jam’iyyar a jihohi kamar su Imo, Delta, Ogun, Rivers da wasu jihohi duk sun shigar da kara kotu domin kalubalantar yadda aka yi musu rashin adalci a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a farkon watan Oktoba.

Asali: Depositphotos
Kakakin jam’iyyar APC na kasa, Lanre-Issa Onilu, ya bayyana a ranar Litinin, 19 ga watan Nuwamba cewa gaggawar garzayawa kotu ba ita ce hanyar neman warware matsala ba, domin jama’iyya ta na da kwamitin ta na sasantawa da warware matsalolin da suka shafin jam’iyya.
Ya ce abin da suka yi ba wani abu ba ne, sai saba wa jam’iyya da kuma rashin da’a. Ya kara da cewa yi wa jam’iyya kafar-ungulu ne, domin kararrakin da suka kai ya saba da dokokin jam’iyyar APC.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Za’a yi zaben gwamna, da na majalisar jiha a ranar 2 ga watan Maris - INEC
Daga nan sai ya shawarce su da su janye kararrakin da suka kai, ko kuma jam’iyyar ta dauki mataki a kan su.
Ya ce janyewar ta su zai sa su ci gajiyar sasanyawar da kwamiti ya fara domin a dinke duk wata baraka a yanzu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng