Dilolin miyagun kwayoyi sun afka kogin Niger a kokarinsu na tserewa jami'an NDLEA
- Wani yunkuri da wasu dilolin miyagun kwayoyi guda biyu suka yi na tserewa jami'an hukumar NDLEA a Lokoja, babban birnin jihar Kogi ya kai ga mutuwarsu
- Wadanda ake zargin, sun fada cikin kogin Niger ne a lokacin da suke kan tserewa jami'an wanda ya sa suka nutse nan take
- Sai dai, an cafke wasu mutane hudu, inda aka bayyana daya a matsayin dila, yayin da ukkun a matsayin masu sayen kwayoyin
Wasu mutane biyu da ake zarginsu da safarar miyagun kwayoyi, sun afka cikin kogin Niger, da ke garin Lokoja, jihar Kogi, a ranar Litinin, 19 ga watan Nuwamba, a kokarin da suke yi na tserewa kamu daga jami'an hukumar NDLEA.
Lamarin dai ya fara ne a lokacin da jami'an hukumar NDLEA, bayan da suka samu rahoto daga al'ummar garin Adankolo da ke Lokoja, suka shiga farautar wadanda ae zargi a yankin. Sai dai, hango jami'an, masu safarar miyagun kwayoyin da masu saye suka ranta a na kare.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa biyu daga cikin wadanda ake zargin sun tsere ne, inda cikin rashin sa'a, suka afka cikin kogin, inda suka shiga cikin komar masu kamun kifi, wanda hakan ya tilastasu nustewa tare da zama silar mutuwarsu.
KARANTA WANNAN: Daga karshe: Kotu ta garkame wanda aka kama yana sojan gona da sunan Kanal

Asali: Depositphotos
Haka zalika, jami'an hukumar na NDLEA sun samu nasarar cakfe, hudu daga cikin wadanda ake zargin, wanda daya daga cikinsu dila ne, yayin da ukkun ke sayen kwayoyin daga wajensa.
Wani mazaunin garin na Adankolo, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce bayan da aka gano gawarwakin mutanen biyu da suka nutse, wasu 'yan ta'adda sun je har ofishin rundunar 'yan sanda sun lalata kayayyakin da ke ciki, a tunaninsu rundunar ce ta yi sanadin mutuwar mutanen biyu.
Ya ce a yanzu haka al'ummar da ke zauna a garin na cikin halin dar-dar, na tunanin ko za a kawo masu hari a kowanne lokaci kamar yadda 'yan ta'addan suka sha alwashin daukar fansar ran 'yan uwansu da suka mutu.
Idrsi Bello, kwamandan rundunar hukumar NDLEA a jihar, wanda ya tabbatar da wannan lamarin ya ce dilan da aka cafke, ana kan tuhumarsa don samun karin bayanai daga wajensa, inda ya ce wadanda ake zargin, za a gurfanar da su kotu da zaran hukumar ta kammala bincike.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng